Kotun ICC ta zubar da dan takarar Nigeria, Jastis Ishaq Bello, bayan ya samu kuri'u 5 cikin 110

Kotun ICC ta zubar da dan takarar Nigeria, Jastis Ishaq Bello, bayan ya samu kuri'u 5 cikin 110

- Babban alkali a babbar kotun tarayya da ke Abuja, Ishaq Usman Bello, ya rasa damar zama alkali a kotun ICC

- A zagaye na farko na zaben da aka gudanar a zagaye na farko, Jastis Bello ya samu kuri'u 12 daga cikin 117 da aka kada

- Amma da aka zo na biyu sai ya samu kuri'u biyar kacal, lamarin da yasa kwamitin bayar da shawarwari ya shawarce shi ya hakura

Ishaq Usman Bello, babban alkali a babbar kotun tarayya da ke Abuja (FCT), ya rasa damar zama alkali a kotun hukunta manyan laifukan ta'addanci da cin zarafi ta kasa da kasa (ICC) da ke Geneva, Switzerland.

Hakan na kunshe ne a cikin sakamakon zaben da aka gudanar ranar Alhamis wanda aka wallafa a shafin yanar gizo na kotun ICC, kamar yadda TheCable ta rawaito.

A watan Yuni na shekarar 2020 ne shugaba Buhari ya zabi Jastis Bello a matsayin dan takarar Najeriya a neman kujerar alkali a kotun ICC.

KARANTA: APC ta dakatar da Sanata Abe da sauran wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar

A zagaye na farko da aka gudanar da zaben neman kujerar, Jastis Bello ya samu kuri'u 12 ne kacal, inda ya zama na biyu a mafi samun karancin kuri'u daga cikin jimillar kuri'u 117 da aka kada.

Kotun ICC ta zubar da takarar Nigeria, Jastis Ishaq Bello, bayan ya samu kuri'u 5 cikin 110
Kotun ICC ta zubar da takarar Nigeria, Jastis Ishaq Bello, bayan ya samu kuri'u 5 cikin 110
Asali: UGC

Da aka sake yin zaben a karo na biyu, Jastis Bello ya samu kuri'u biyar ne kacal daga cikin kuri'u 110 da aka kada.

Tun a cikin watan Oktoba kwamitin bayar da shawara ya nuna alamun ba zai kai ga nasara ba a karshe bayan sun nuna alamun bai samu karbuwa ba.

KARANTA: Muhimman tambayoyi 7 da amsoshinsu a kan rigakafin annobar korona

'Yan takarar kasashen Ingila da Georgia, Korner Joanna da Lordkipanidze Gocha, aka zaba daga cikin 'yan takara 18.

Alkalai shidda ake sa ran zaba domin cika kaso daya cikin uku na jimillar alkalai 18 da kotun keda su.

A kwanakin baya ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa kotun ICC mai tuhumar manyan laifukan ta'addanci da cin zarafin jama'a ta ce za ta binciki hukumomin tsaron Nigeria.

Mai gurfanarwa a kotun ta ce ofishinta ya na kwararan hujjoji na zahiri da za'a iya kimantasu a kan jami'an hukumomin tsaron Nigeria

Fatou Bensouda, mai gurfanarwa da ke shirin barin gado, ta lissafa wasu manyan laifuka da ICC ke zargin jami'an tsaron Nigeria da aikatawa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng