Covid-19: El-Rufa'i ya dauki sabon mataki da ya shafi ma'aikata, Masallatai da Coci

Covid-19: El-Rufa'i ya dauki sabon mataki da ya shafi ma'aikata, Masallatai da Coci

- Gwamnatin jihar Kaduna ta kara dauki mataki na gaba bayan sanar da rufe makarantu da wuraren taron biki da gidajen rawa

- A wani sako da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya fitar ya sanar da cewa ma'aikata kasa da mataki na 14 su cigaba da zama a gida

- Kaduna na daga cikin jihohin da ake ake samun hauhawar alkaluman masu kamuwa da korona a kowacce rana a 'yan kwanakin baya bayan nan

A makon da ya gabata ne Legit.ng ta wallafa rahotanni a kan wasu jihohi da suka sanar da rufe makarantun firamare da sakandire saboda fargabar dawowar annobar cutar korona a karo na biyu.

Gwamnatin jihar Kaduna ce ta fara fitar da sanarwar cewa ta rufe makarantu kafin daga bisani ta sanar da cewa ta bayar da umarni rufe wuraren taron bikin da gidajen rawar disko.

A cewar El-Rufa'i, "bugu da kari a kan matakan da aka dauka a makon da ya gabata, gwamnatin jihar Kaduna (KDSG) ta umarci ma'aikata daga kasa da mataki na agidajensu daga ranar Litinin, 21 ga watan Disamba.

KARANTA: CBN za ta fara rabawa masu kiwon kaji da tsuntsaye tallafin biliyan N12.8

"Gwamnatin jihar Kaduna ta na kira ga mazauna jihar akan su kula tare da kara da lura da biyayya ga dukkan matakan kare kai daga kamuwa da yada kwayar cutar korona, yin hakan alhakin kowa da kowa ne."

Wani bangare na sanarwar ya bukaci Masallatai da Cocinan jihar Kaduna su tanadi ruwa da sinadaran tsaftace hannu tare da tabbatar da nesantar juna da amfani da takunkumin fuska a lokutan bauta.

A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da umarnin rufe dukkan wasu wuraren taron biki, gidajen rawar disko, da cibiyoyin motsa jiki, a wani yunkuri na dakile yaduwar kwayar cutar korona a karo na biyu.

KARANTA: Babban Sufetan ƴan sanda na ƙasa ya bada umarnin baza jami'an rundunar SWAT da suka maye gurbin SARS

Kazalika, gwamnatin ta takaita harkokin wuraren sayar da abinci; babu zama a ci, sai dai a kunshewa mutum abincinsa ya tafi da shi, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Dawowar korona: El-Rufa'i y umarci rukunin wasu ma'aikata su fara aiki daga gida daga Litinin
Dawowar korona: El-Rufa'i y umarci rukunin wasu ma'aikata su fara aiki daga gida daga Litinin @KDSGov
Asali: Twitter

Bugu da kari, an umarci direbobi su rage yawan mutane da kaso 50 tare da tabbatar da cewa duk fasinjoji sun saka takunmi da kuma tabbatar da nesantar juna.

A baya Legit.ng Hausa ta wallafa cewa ta samo muku wasu ingantattun bayanai da muhimmam tambayoyi da amsoshinsu da ya kamata kowanne ɗan Najeriya ya sani dangane da rigakafin cutar korona.

Alamu sun tabbatar da samun sauki daga wannan magani duk da cewa cutar na neman sake dawowa a karo na biyu.

Sai dai duk da haka, riga-kafin na iya kare mutum daga sake kamuwa da cutar duk da akwai alamun tambayoyi kan hakan

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng