FG: CBN za ta fara rabawa masu kiwon kaji da tsuntsaye tallafin biliyan N12.8

FG: CBN za ta fara rabawa masu kiwon kaji da tsuntsaye tallafin biliyan N12.8

- Manoman kaji da kiwon tsuntsaye zasu dara, a cewar babban bankin kasa (CBN)

- CBN ya ce an ware zunzurutun kudi Naira biliyan N12.55 domin tallafawa masu kiwon kaji

- A cewar babban bankin, hakan na daga cikin tsarin gwamnati na bunkasa samar da kwai, naman kaji, da ayyuka ga mata da matasa

Babban bankin ƙasa CBN, ya fitar da zunzurutun kuɗi Naira biliyan N12.55 domin tallafawa masu kiwon kaji, a wani yunƙurin gwamnati na ƙara bunƙasa samar da ƙwai da naman kaji tare da samar da ayyukan yi a ƙasa baki ɗaya.

Bayanai daga bankin CBN sun nuna cewa an fitar da kuɗin ne tsakanin watannin ƙarshe na shekarar 2019 zuwa watan Nuwamba na shekarar 2020, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Daraktan gudanarwa a bangaren sha'anin kuɗi, Philip Yila Yusuf, ya tabbatar da haka inda ya ƙara da cewa ana kan tsare-tsaren bayar da rancen kuɗaɗen sakamakon ƙaruwar masu kiwon kajin da ake samu.

Bugu da ƙari, kuɗaɗen za'a rarraba su ne ga manoma kiwon kajin kafin ƙarshen wannan shekarar 2020.

FG: CBN za ta fara rabawa masu kiwon kaji da tsuntsaye tallafin biliyan N12.8
FG: CBN za ta fara rabawa masu kiwon kaji da tsuntsaye tallafin biliyan N12.8 @Daily_trust
Source: Twitter

Bayanai daga babban bankin na ƙasa ya kara nuna cewa, masu kiwon kajin an ware musu Naira biliyan 12.55 zuwa ga ƙananun bankuna da kuma bankin NIRSAL.

CBN ta bayyana cewa manoman kaji 639 da suka nemi tallafi a karkashin tsarin AGMEIS, sun karbi biliyan 1.996 daga Bankin NIRSAL da ke fadin Najeriya.

Haka zalika an raba biliyan 1.59 ga manoma 898 a wani tsari na farfaɗowa daga bugun korona, a cewar babban bankin.

A baya Legit.ng Hausa ta rawaito cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarnin bude iyakokin kan tudu guda hudu daga ranar 31 ga watan Disamba, 2020.

Ministar kudi, Zainab Ahmed, ce ta sanar da hakan ranar Laraba yayin ganawarta da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC).

Iyakokin guda hudu da za'a bude sune kamar haka: Illela a Jihar Sokoto, Maigatari a jihar Jigawa, dukkansu a arewacin Nigeria. Sai kuma iyakar Seme da ke Legas, yankin kudu maso yamma, da iyakar Mfun da ke yankin kudu maso kudu.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel