Wasu kananan yara ne rike da manyan bindigogi: Yaran da ya bayyana a bidiyon Shekau ya yi magana bayan kubuta

Wasu kananan yara ne rike da manyan bindigogi: Yaran da ya bayyana a bidiyon Shekau ya yi magana bayan kubuta

- Dalibin da ya bayyana a bidiyon Shekau ya yi magana kan abinda ya faru

- Ya fadi yadda yan ta'addan suka umurceshi ya fadi abubuwan da ya fadi

Daya daga cikin daliban makarantar gwamnatin GGSS Kankara, a jihar Katsina, ya yi bayani abubuwan da suka fuskanta cikin kwanaki shidan da suka yi hannun yan bindiga.

Dalibin, wanda yayi ikirarin cewa shi ya bayyana a bidiyon da Boko Haram ta saki ranar Alhamis, ya ce yan bindigan ne suka fada masa abubuwan da ya furta bidiyon.

"Su suka ce in fadi su yan Boko Haram ne - yan bangaren Abu Shekau," ya fadi.

"Abinda na fahimta shine ba yan Boko Haram bane."

Yaran wanda yayi magana da tashar Arise TV kuma Legit ta saurara ya kara da cewa, "maganar gaskiya, barayin sun firgita lokacin da suka ga jirage. Su suka sani inyi magana a bibiyon don fadawa gwamnati su daina turo jirage, idan ba haka ba zasu kashemu."

"Mun sha bakar wahala, suna dukanmu dare da rana. Sau daya suke bamu abinci a rana."

"Wasu daga cikinsu yara ne kawai da manyan bindigogi."

KU KARANTA: Yan Boko Haram sun yi garkuwa da fasinjoji 35 a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri

Wasu kananan yara ne rike da manyan bindigogi: Yaran da ya bayyana a bidiyon Shekau ya yi magana bayan kubuta
Wasu kananan yara ne rike da manyan bindigogi: Yaran da ya bayyana a bidiyon Shekau ya yi magana bayan kubuta Credit: Punch.com
Asali: UGC

DUBA: Matasan Kataf sun yi martani, sun halaka mace 1 da yara 6 a Kaduna

Mun kawo muku cewa a ranar Alhamis, 17 ga wata aka sako daliban makarantar sakandaren kimiya dake Kankara akalla 340 yanzu.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sanar da hakan.

A ranar Juma'a 11 ga wata ne 'yan bindiga suka afka GSSS Kankara da ke jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da daruruwan dalibai makarantar, bayan isar Shugaba Muhammadu Buhari Daura, garinsa na haihuwa da sa'o'i kadan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel