Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai hadu da daliban Kankara 344 da aka sako

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai hadu da daliban Kankara 344 da aka sako

- Bayan mako guda hannun yan bindiga, an sako dalibai 344 na makarantar Kankara

- Shugaba Buhari ya yi laale marhabun da wannan nasara da gwamnatin ta samu

- Zai gana da su kafin komawa birnin tarayya Abuja

Shugaba Muhammadu Buhari zai gana da daliban makarantar Kankara misalin karfe 3 na rana yau Juma'a, 18 ga Disamba, 2020.

The Cable ta ruwaito cewa sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa, ya bayyana hakan ta mai magana da yawunsa.

Buhari zai gana da su ne a gidan gwamnatin jihar Katsina.

A jiya Shugaba Muhammadu Buhari ya yi maraba da sakin daliban makarantar GGSS Kankara a jihar Katsina, mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.

Buhari ya siffanta cetonsu a matsayin babban sauki ga iyayensu, kasar, da kuma duniya gaba daya.

A gajeren jawabin da ya yi bayan sanar da sakin yaran, Buhari ya mika godiyarsa ga dukkan wadanda ke da hannu wajen wannan nasara.

KU DUBA: Sau daya suka bamu abinci cikin kwanaki 2, inda muke barci muke bahaya: Daya daga cikin yaran Kankara

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai hadu da daliban Kankara 344 da aka sako
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai hadu da daliban Kankara 344 da aka sako CREDIT: FEMI ADESINA
Source: Facebook

KU DUBA: Hotunan 'yan makarantar Kankara suna isa gidan gwamnatin Katsina

Mun kawo muku cewa daliban GSSS Kankara na jihar Katsina da 'yan bindiga suka sace sun iso gidan gwamnati.

Jami'an tsaro ne suka yi musu iso har cikin gidan gwamnatin jihar Katsina.

A ranar Alhamis, 17 ga wata aka sako daliban makarantar sakandaren kimiya dake Kankara akalla 340 yanzu.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sanar da hakan.

A ranar Juma'a 11 ga wata ne 'yan bindiga suka afka GSSS Kankara da ke jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da daruruwan dalibai makarantar, bayan isar Shugaba Muhammadu Buhari Daura, garinsa na haihuwa da sa'o'i kadan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel