Yan Boko Haram sun yi garkuwa da fasinjoji 35 a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri

Yan Boko Haram sun yi garkuwa da fasinjoji 35 a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri

- Mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da wasu fasinjoji guda 35 a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri

- Wasu majiyoyi na sojoji ne suka bayyana afkuwar lamarin a ranar Juma'a

- Sai dai wani babban jami'in dan sanda a Maiduguri ya ce an ceto 10 daga cikinsu

Akalla matafiya 35 ne yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da su a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

Majiyoyin soji wadanda suka bayyana lamarin ga jaridar The Cable sun bayyana cewa yan ta’addan sun far ma ayarin matafiyan a kusa da Garin Kuturu da ke Jakana da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Juma’a.

An tattaro cewa yan ta'addan wadanda suka kasance cikin kayan sojoji, sun sanya shinge a babbar titin da motocin Hilux guda biyar kafin suka tafi da fasinjojin.

Yan Boko Haram sun yi garkuwa da fasinjoji 35 a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri
Yan Boko Haram sun yi garkuwa da fasinjoji 35 a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

“Fasinjojin sun fara gano wuta na ci, amma sai suka zata ana kona jeji ne, ba tare da sanin cewa an rigada an farma wani direban babban motan Dangote bane sannan aka cinna masa wuta,” in ji wata majiya.

KU KARANTA KUMA: Maina: Irin rayuwar da nayi a kurkuku tsawon kwanaki 5, Ndume

“Amma a yayinda suke tunkarar wajen, sai suka ga yan ta’addan suna tunkaro su a manyan motoci dauke da muggan makamai, kafin su juya motocinsu don tserewa, tuni yan ta’addan suka cimma su.

“Fasinjoji da dama sun tsere cikin jeji, anyi garkuwa da mutum 35, aan cina wa wasu motoci masu zaman kansu biyu da babbar mota daya wuta. An kuma yasar da motoci tara na fasinjojin da aka sace a wajen yayinda aka sace kayayyakinsu.”

Wani babban jami’in dan sanda daga tawagar rundunar da ke Maiduguri wanda ya nemi a boye sunansa ya ce an ceto fasinjoji 10 yayinda aka kwashi wadanda suka jikkata zuwa asibitin kwararru da ke Maiduguri don jinya.

KU KARANTA KUMA: Ba za a yi zabe ba a 2023, Jigon arewa Yusuf ya kaddamar

A wani labarin, Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno ya naɗa, mafarauciya, A'isha Gombi mai bashi shawara.

Zulum ya naɗa ta mai bada shawara kan yaƙi da ta'addanci ne don gudunmawa da jarumtar ta a yaƙi da ta'addanci.

Zulum ya bukaci ta zage damtse ta kuma cigaba da aikin tuƙuru kamar yadda aka santa don cimma manufofin gwamnatin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel