Matasan Kataf sun yi martani, sun halaka mace 1 da yara 6 a Kaduna

Matasan Kataf sun yi martani, sun halaka mace 1 da yara 6 a Kaduna

- Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutane 6 a wani hari na karamar hukumar Kauru

- Kamar yadda suka tabbatar, harin na mayar da martani ne bayan harin ranar Alhamis da aka kai Zangon Kataf

- Harin da aka kai ranar Alhamis a kauyen Gora Gan, na Zangon Kataf yayi sanadiyyar mutuwar mutane 7

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutane 6, da wata mata tare da wasu yara 6 a wani hari na mayar da martani a karamar hukumar Kauru, bayan harin Zangon Kataf da aka kai ranar Alhamis.

Idan ba a manta ba, daren Alhamis, 'yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Zangon Kataf dake jihar Kaduna, inda suka kashe mutane 7.

A wata takarda da kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro, Samuel Aruwan, ya ce gwamnatin tace a karkashin taimakon rundunar Operation Safe Heaven da 'yan sanda, sun tabbatar wa da gwamnatin jihar Kaduna cewa rikicin ya faru ne tsakanin makiyayan Kauru da karamar hukumar Lere.

KU KARANTA: Matashiya mai kunar bakin wake ta tada bam, ta kashe mutum 3 a Borno

Matasan Kataf sun yi martani, sun halaka mace 1 da yara 6 a Kaduna
Matasan Kataf sun yi martani, sun halaka mace 1 da yara 6 a Kaduna. Hoto daga @daily_nigerian
Source: Twitter

A cewar Aruwan, wasu 'yan daban matasa ne suka kai harin, bayan kashe mutane 7 da aka yi da daren Alhamis a Gora Gan, karamar hukumar Zangon Kataf.

"Jami'an tsaro sun tabbatar da kisan makiyaya 7 a Unguwan Idi da kauyen Kasheku da ke karamar hukumar Kauru, sai kuma wasu makiyaya 2 da aka ji wa munanan raunuka a kauyen Ningi da ke karamar hukumar Lere.

Aruwan ya ce an kashe makiyaya 7 a Unguwan Idi da kauyen Kasheku da ke karamar hukumar Kauru, Mustapha Haruna (Mai shekara 1), Ya'u Kada (shekara 1), Sa'idu Abdullahi (shekara 1), Zainab Zakari (shekara 1), Sadiya Abdullahi (shekaru 5), Aisha Abdullahi (shekara 1) da kuma wata mata, wacce aka kasa ganeta saboda kuna.

Kwamishinan ya ce har yanzu ba a ga mutane 5 ba, kuma har yanzu rundunar tana cigaba da neman su. Ya kara da cewa, a harin, har kona bukkoki 6 sukayi.

KU KARANTA: Mu ne muka ceto yaran Kankara, Sojin Najeriya sun musanta ikirarin Gwamnoni da Miyetti Allah

A wani labari na daban, Gwamna Bello Matwalle na jihar Zamfara ya caccaki jam'iyyar APC a kan zarginsa da daukar nauyin ta'addanci a arewa maso yammacin kasar nan.

Idan ba a manta ba, satar daliban GSSS Kankara jihar Katsina, jam'iyyar APC ta yi zargin gwamnan PDP da kasancewa mai ruwa da tsaki a kan ta'addanci a arewa maso yamma.

Bayan jin hakan, gwamnan ya saki wata takarda, ta hannun mai bashi shawara a kan harkar labarai, Zailani Bappa, inda yace kame-kame kawai jam'iyyar take yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel