Mu ne muka ceto yaran Kankara, Sojin Najeriya sun musanta ikirarin Gwamnoni da Miyetti Allah

Mu ne muka ceto yaran Kankara, Sojin Najeriya sun musanta ikirarin Gwamnoni da Miyetti Allah

- Duk da gwamnan jihar Katsina da na Zamfara sun ce kungiyar makiyaya shanu ta Miyetti Allah ce ta taka rawa wurin ceto dalibai 344 na Kankara

- A wata takarda ta ranar Juma'a, kakakin rundunar soji, John Enenche ya ce rundunar Operation Hadarin Daji ce ta ceto yaran

- Kamar yadda Enenche yace, rundunar ta yi amfani da dabara da kwarewa ta musamman wurin tabbatar da ceto da yaran da ransu

Hedkwatar tsaro ta ce rundunar Operation Hadarin Daji ta samu nasarar ceto daliban GSSS Kankara guda 344 na jihar Katsina, The Cable ta wallafa.

Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara da Bello Masari, takwaransa na jihar Katsina sun ce kungiyar makiyaya shanu ra Miyetti Allah sune suka taka babbar rawa wurin ceto daliban.

Amma a wata takarda ta ranar Juma'a, kakakin hedkwatar tsaro, John Enenche, ya ce rundunar ce take da alhakin ceto yaran. A cewarsa, rundunar ta yi godiya ga jama'a musamman wadanda suka samar mu su da labaran da suka taimaka wurin ceto yaran.

Mu ne muka ceto yaran Kankara, Sojin Najeriya sun musanta ikirarin Gwamnoni da Miyetti Allah
Mu ne muka ceto yaran Kankara, Sojin Najeriya sun musanta ikirarin Gwamnoni da Miyetti Allah. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kankara: 'Yan bindiga da suka sace yaran makaranta suna tattaunawa da Miyetti Allah, Masari

A cewarsa, rundunar jaruman ce ta samu nasarar ceto daliban ta hanyar amfani da dabara ta musamman don tabbatar da ceto su da rayukansu.

"Kamar yadda muka dauki alkawarin tabbatar da mun ceto daliban GSSS Kankara da ke jihar Katsina, rundunar Operation Hadarin Daji ta ceto daliban 344 a ranar Alhamis, 17 ga watan Disamban 2020," a cewarsa.

"Rundunar soji ta kasa, ta yaba wa rundunar Operation Hadarin Daji, tare da duk sauran jami'an tsaro saboda dagewarsu da amfani da kwarewarsu."

KU KARANTA: Fusatattun matasa sun banka wa barawon waya wuta a Oyo

A wani labari na daban, babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya cire duk shugabannin tsaro a kan gaza samar wa da kasa tsaro bisa kararsa da aka kai kotun.

Korafin da dan takarar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam'iyyar AAC, Alhaji Said Uba, yayi, inda ya nemi shugaba Buhari yayi gaggawar daukar mataki, don ya gaza kulawa da dukiyoyi da rayukan 'yan Najeriya, Vanguard ta wallafa.

Sauran wadanda suka shiga karar sun hada da Antoni janar na kasa, majalisar tarayya, shugaban majalisar dattawa, shugaban rundunar sojin kasa, shugaban sojojin ruwa, shugaban sojojin sama da kuma sifeta janar na 'yan sanda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel