Kankara: 'Yan bindiga da suka sace yaran makaranta suna tattaunawa da Miyetti Allah, Masari

Kankara: 'Yan bindiga da suka sace yaran makaranta suna tattaunawa da Miyetti Allah, Masari

- Gwamna Masari na jihar Katsina ya ce an fara tattaunawa da 'yan bindigan don ceto daliban GSSS Kankara

- A cewar gwamnan, an fara daidaitawa dasu ta kungiyar masu kiwon shanu ta Miyetti Allah ta Najeriya, MACBAN

- Ya tabbatar wa da iyayen daliban cewa yaransu suna nan cikin koshin lafiya kuma a raye, kada su damu

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya ce ana tattaunawa da 'yan bindigan da suka sace daliban GSSS Kankara ta Kungiyar masu kiwon shanu ta Miyetti Allah ta Najeriya, MACBAN.

A kalla 17 daga cikin daliban sun tsere daga wurin masu garkuwa da mutanen, kuma sun koma wurin iyayensu. Ya musanta batun mutuwar wani daga cikin daliban.

Sannan jami'an tsaro da wasu majiyoyi sun sanar da AFP cewa Boko Haram ne suka horar da wasu 'yan bindiga don su sace daruruwan daliban GSSS Kankara, jihar Katsina.

Kankara: 'Yan bindiga da suka sace yaran makaranta suna tattaunawa da Miyetti Allah, Masari
Kankara: 'Yan bindiga da suka sace yaran makaranta suna tattaunawa da Miyetti Allah, Masari. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan sanda sun sake damke mutumin da yayi bidiyon da ya tada zanga-zangar EndSARS

Dama 'yan Boko Haram sun ce sune suke da alhakin sace daliban sama da 300, Vanguard ta wallafa.

Wannan maganar ta gwamnan ta zo ne bayan iyayen daliban sun lashi takobin cewa za su cigaba da zama cikin makarantar har sai yaransu sun koma gidajensu lafiya.

A wani bangaren kuma, CAN ta bayyana satar yaran a matsayin wani salo na daban wanda 'yan bindiga suka fara bi, don ganin sun hana 'yan Najeriya zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sannan kuma CNG ta yada zango a jihar Katsina, don fara zanga-zangar lumana da nuna damuwarsu don gwamnati tayi gaggawar neman hanyar ceto yaran.

KU KARANTA: Yadda 'yan sanda suka dinga yi wa mutumin da aka sace wa mota dariya

A wani labari na daban, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya shawarci matasan jiharsa da su yaki 'yan ta'adda da 'yan fashi kada su tsaya jiran hukuma.

Gwamnan ya bayar da wannan shawarar ne bayan wasu 'yan ta'adda sun afka wa kauyen Agboughul da ke wajen Makurdi da misalin karfe 11pm, inda suka kashe wani lauya, Moses Udam, wanda fasto ne a Gospel Faith Mission, matarsa Nkechi da wani tsohon makaho, Mazugu Nyikor, mai shekaru 88.

An tsinci gawar mata da mijin, sannan sun ji wa yaran Nyikor 2, ciwo da alburusai, sannan sun tsere da kanwar faston, inda suka bukaci N200,000 a matsayin kudin fansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng