Rashin tsaro: An maka Buhari a gaban kotu saboda rashin sallamar shugabannin tsaro

Rashin tsaro: An maka Buhari a gaban kotu saboda rashin sallamar shugabannin tsaro

- Dan takarar gwamnan jihar Adamawa karkashin jam'iyyar AAC, Alhaji Said Uba ya maka Buhari a kotu

- Ya kai kararsa ne babbar kotun tarayya da ke Abuja, bisa kin sauke shugabannin tsaron Najeriya

- Uba ya bukaci kotu ta tilasta Buhari ya biya wadanda matsalar rashin tsaro ya shafa N100,000,000,000

Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya cire duk shugabannin tsaro a kan gaza samar wa da kasa tsaro bisa kararsa da aka kai kotun.

Korafin da dan takarar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam'iyyar AAC, Alhaji Said Uba, yayi, inda ya nemi shugaba Buhari yayi gaggawar daukar mataki, don ya gaza kulawa da dukiyoyi da rayukan 'yan Najeriya, Vanguard ta wallafa.

Sauran wadanda suka shiga karar sun hada da Antoni janar na kasa, majalisar tarayya, shugaban majalisar dattawa, shugaban rundunar sojin kasa, shugaban sojojin ruwa, shugaban sojojin sama da kuma sifeta janar na 'yan sanda.

KU KARANTA: Kankara: 'Yan bindiga da suka sace yaran makaranta suna tattaunawa da Miyetti Allah, Masari

Rashin tsaro: An maka Buhari a gaban kotu saboda rashin sallamar shugabannin tsaro
Rashin tsaro: An maka Buhari a gaban kotu saboda rashin sallamar shugabannin tsaro. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Uba, wanda ya maka Buhari a kotun a maimakon wadanda matsalar rashin tsaro ta shafa a arewacin Najeriya, ya kuma bukaci Buhari ya biya wadanda al'amarin ya shafa N100,000,000,000.

Ya bukaci kotu ta tilasta Buhari ya sauke shugabannin tsaro saboda rashin bai wa kasa tsaro. Kuma su yi gaggawar rubuta wasikar bayar da hakuri ga 'yan Najeriya cikin kwanaki 7.

Sannan ya bukaci a biya N100,000,000,000 ga wadanda al'amarin ya shafa. Inda ya bayyana yadda mutane da dama suka rasa gidaje, iyalai da dukiyoyin da suka mallaka sanadiyyar rashin tsaro.

KU KARANTA: Budurwa mai shekaru 24 ta aura jakar da ta yi soyayya da ita na shekaru 5

A wani labari na daban, Gwamna Bello Masari na jihar Katsina ya ce wadanda suka sace daliban GSSS Kankara, masu garkuwa da mutane ne ba 'yan Boko Haram ba, Channels Tv ta wallafa.

Ya musanta maganar Shekau ne a ranar Laraba, inda yace kowa yasan cewa 'yan bindigan gargajiya ne suka sace dalibannan.

Bayan kwanaki kadan da wasu 'yan ta'adda suka sace daliban GSSS Kankara, sai ga wata murya ta fara yawo a kafafen sada zumuntar zamani, wacce take cewa, "Ni ne Abubakar Shekau kuma 'yan uwana ne suke da alhakin sace yaran Katsina."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel