Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar plateau, Simon Lalong, ya kamu da Korona
- Alamu na nuni da cewa da gaske annobar korona ta sake yunkurowa a karo na biyu
- Alkaluman masu kamuwa da kwayar cutar sai kara hawan gwauron zabi suke yi a 'yan kwanakin baya bayan nan
Gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong, ya harbu da muguwar cutar nan ta Coronavirus.
Diraktan yada labaran gwamnan Dr Makut Macham, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Alhamis, Channels TV ta samu.
Ya yi bayanin cewa gwamnan da iyalansa aka yiwa gwajin amma shi kadai ya kamu cikinsu.
Tuni an killace shi kuma za a gwada hadimansa na jiki
KU KARANTA: Shugaban kasan Faransa, Emmanuel Macron ya kamu da cutar Korona
Gabanin Lalong, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya kamu da cutar Korona yau Asabar, 12 ga watan Disamba, 2020.
Daya daga cikin hadimansa, Jubrin Gawat, ya bayyana hakan yau Asabar, 12 ga watan Disamba, 2020.
Hakazalika kwamishana kiwon lafiyan jihar Legas, Akin Abayomi, ya saki jawabi kan kamuwar gwamnan.
A jawabin da ya saki da yammacin nan yace sakamakon gwajin da aka yiwa gwamnan ranar Juma'a, ya tabbata cewa ya kamu da cutar.
"Gwamna na jinya a gidansa kuma manyan kwararrun likitoci daga asibitin IDH Yaba na kula da shi," Abayomi yace.
KU DUBA: Bidiyon amarya da ango rai bace ana musu liki a yayin bikinsu ya janyo cece-kuce
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng