Bidiyon amarya da ango rai bace ana musu liki a yayin bikinsu ya janyo cece-kuce
- Kowa ya san yadda ma'aurata suke shiga shauki da matukar farinciki a ranar aurensu
- Amma bayyanar wannan bidiyon a kafar sada zumunta, mutane da dama suka yi ta tsokaci iri-iri
- Bidiyon ya nuna yadda angon da amaryarsa suka sunkuyar da fuskoki cikin takaici, abokai suna manna musu N10
Wani bidiyon amarya da ango wanda 'yan uwa da abokan arzikinsu suka yi ta manna musu N10 ya yi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, shafin Linda Ikeji ya wallafa.
Bidiyon wanda 'yan Najeriya da dama suka yi ta cewa da alama ma'auratan basa yin farinciki da bikin.
Kowa yana tunanin dalilin da zai hanasu murna ranar aurensu, wasu cewa suke yi saboda N10 da ake manna musu ne, wasu kuma suna zargin auren dole ne.
KU KARANTA: Kankara: 'Yan makaranta da aka sace suna cikin koshin lafiya, Sojin Najeriya
Bidiyon ya nuna yadda ma'auratan suka sunkuyar da kawunansu kasa, abokan arziki suna watsa musu kudade. Maimakon a gan su cikin farinciki, sai aka ga akasin hakan.
Wata blessed_beautiful_queen cewa tayi, "Da alama N10 da ake manna musu ne ta fusata su, da a ce a kalla N1000 aka manna wa angon, na tabbatar zai yi murmushi."
Wata basilling1 cewa tayi, "Mugayen abokai"
Oseh1 kuwa cewa yayi, "Kalli wata mugunta, koda yake gara da aka manna musu N10, maimakon a barsu haka nan."
KU KARANTA: Kankara: Masari ya caccaki Shekau, ya ce 'yan makaranta na hannun 'yan bindiga
A wani labari na daban, wata mata ta bayyana yadda ta fada kogin soyayya da wata jaka, kuma har ta kai ga auren jakar. Rain Gordon ta ce kullum soyayyar jakar tana ratsa zuciyarta kuma hakan ya girma ya koma sha'awa.
A watan Yunin wannan shekarar ne ta bayyana aurenta da jakar, wacce ta sanya wa suna Gideon.
Matar mai shekaru 24 ta ce duk da a baya tayi soyayya da samari da dama, amma tafi jindadin soyayya da abubuwa marasa rai.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng