Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu ya kamu da cutar Korona

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu ya kamu da cutar Korona

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya kamu da cutar Korona yau Asabar, 12 ga watan Disamba, 2020.

Daya daga cikin hadimansa, Jubrin Gawat, ya bayyana hakan yau Asabar, 12 ga watan Disamba, 2020.

Hakazalika kwamishana kiwon lafiyan jihar Legas, Akin Abayomi, ya saki jawabi kan kamuwar gwamnan.

A jawabin da ya saki da yammacin nan yace sakamakon gwajin da aka yiwa gwamnan ranar Juma'a, ya tabbata cewa ya kamu da cutar.

"Gwamna na jinya a gidansa kuma manyan kwararrun likitoci daga asibitin IDH Yaba na kula da shi," Abayomi yace.

"Sanwo-Olu yana cikin koshin lafiya a kwance kuma muna kyautata zaton cewa zai warke ba tare da bata lokaci ba."

"Muna fuskantar hauhawar adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a jihar Legas."

KU KARANTA: Ana artabu tsakanin da yan Boko Haram a Askira Uba

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu ya kamu da cutar Korona
Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu ya kamu da cutar Korona
Asali: Twitter

A jiya mun kawo muku cewa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, zai shiga killace kansa, bayan daya daga cikin hadimansa na jiki ya kamu da cutar Korona ranar Alhamis.

Za'a yiwa gwamna Sanwo-Olu da mambobin majalisarsa gwajin cutar Korona ranar Juma'a amma zai cigaba da killace kansa kar lokacin da sakamakon ya fito.

"Muna fuskantar hauhawar adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a jihar Legas kuma dukkan al'ummar jihar su bi ka'idojin baiwa juna tazara, tsaftace hannu da kuma gujewa taron jama'a," kwamishanan lafiyan jihar, Akin Abayomi yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel