Yanzu-yanzu: Shugaban kasan Faransa, Emmanuel Macron ya kamu da cutar Korona

Yanzu-yanzu: Shugaban kasan Faransa, Emmanuel Macron ya kamu da cutar Korona

- Bayan fama da kalubale wajen shugabannin kasashen Musulmai, Macron ya fadi rashin lafiya

- Ya shiga jerin su Donald Trump, dake shirin sauka daga mulki a Junairu

Shugaban kasan Faransa, Emmanuel Macron, ya kamu da cutar COVID-19, fadar shugaban kasa ta bayyana, kuma tuni ya shiga killace kansa na mako mai zuwa.

"Shugaban kasa ya kamu da COVID-19 yau." fadar ta bayyana a wani jawabi.

Bisa ga sharrudan da kasar ta gindaya, Macron "zai killace kansa na tsawon makonni bakwai. Zai cigaba da aiki da harkokinsa daga cikin gida," ta kara.

Shugaban Faransa ya shiga cikin jerin shugabannin kasa a duniya da suka kamu da muguwar cutar.

Daga cikin wadanda suka kamu a baya sun hada da Firai Ministan Birtaniya, Boris Johnson da shugaban kasar Amurka, Donald Trump.

Sama da mutane 59,300 suka mutu sanadiyar cutar Coronavirus a kasar Faransa, bisa alkaluman hukumomin lafiyar kasar.

KU KARANTA: Bayan kashe N28bn kan Korona, ministan Abuja ya ce ta dawo kuma ta fi hadari yanzu

Yanzu-yanzu: Shugaban kasan Faransa, Emmanuel Macron ya kamu da cutar Korona
Yanzu-yanzu: Shugaban kasan Faransa, Emmanuel Macron ya kamu da cutar Korona
Asali: Original

KU KARANTA: Gwamnan Legas ya bada umurnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandaren jihar

A Najeriya kuwa, mutane 930 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Laraba, 16 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Alhamis ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 75,062 a Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel