Tsohon shugaban bangare na APC a Edo da magoya bayansa sun koma PDP

Tsohon shugaban bangare na APC a Edo da magoya bayansa sun koma PDP

- Jam'iyyar APC ta sake rasa wasu mambobinta da dama bayan shan kaye da ta yi a zaben gwamna da ya gabata

- Hakan na zuwa ne bayan, Ojezua, tsohon shugaban jam'iyyar ta jagoranci magoya bayansa sun koma jam'iyyar PDP mai mulki a jihar

- Ojezua ya lissafa dalilai biyu da suka saka shi ya fice daga jam'iyyar APC ya koma PDP mai mulki a jihar

Anselm Ojezua, tsohon wani sashi na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Edo, ya koma jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

The Sun ta ruwaito cewa Ojezua ya jagoranci wasu mambobin jam'iyyar ta APC zuwa PDP inda ya ce ya fice ne saboda rashin gamsuwa da kamun ludayin shugabannin jam'iyyar na kasa.

Tsohon shugaban bangare na APC a Edo da magoya bayansa sun koma PDP
Tsohon shugaban bangare na APC a Edo da magoya bayansa sun koma PDP. @EdostateAPC
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An kama Bishop na coci yana lalata da matar wani faston da ke ƙarƙashinsa

Tsohon jigon na APC ya kuma ce rashin bin dokokin kundin tsarin mulkin jam'iyyar da shugabannin jam'iyyar ba su yi shima dalili ne da yasa ya fice daga jam'iyyar.

Legit.ng ta tattaro cewa ya yanke shawarar komawa jam'iyyar ta PDP ne yayin wani babban taro na wani sashi na shugabannin jam'iyyar, SEC, da aka gudanar a ranar Laraba, 16 ga watan Disamba a Benin City.

KU KARANTA: Ina fuskantar matsin lamba akan sai na binciki gwamnatocin baya, Gwamnan Bauchi

Bayan cimma matsaya yayin taron da aka yi da Ojezua da shugabannin kananan hukumomi 18 na jihar, sun shawarci magoya bayan jam'iyyar fiye da 150,000 su koma PDP tare da su.

Wasu sashi na sakon ya ce;

"Mun saka hannu kan yarjejeniyar cewa shugabannin bangaren mu na jam'iyyar karkashin jagorancin Ojezua da shugabannin a kananan hukumomi 18 za mu koma PDP mu hadu da mai girma Mista Godwin Nogheghase Obaseki da mataimakinsa, Hon. Philip Shuaibu."

A wani labarin, gwamnatin tarayyar Najeriya, a ranar Lahadi ta ce shirin samar da ayyuka na musamman, SPW, guda 774,000 zai fara ne a ranar 5 ga watan Janairun shekarar 2021.

Karamin ministan Kwadago da samar da ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ne ya shaidawa The Nation hakan ranar Lahadi a Abuja.

Shirin samar da ayyukan ga masu sana'o'in hannu na watanni uku inda za a rika biyansu N20,000 duk wata ya samu tsaiko sakamakon rashin jituwa tsakanin ministan da tsohon shugaban hukumar samar da ayyuka ta kasa, NDE, Nasir Ladan da Buhari ya sallama daga aiki makon data gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel