An kama Bishop na coci yana lalata da matar wani faston da ke ƙarƙashinsa

An kama Bishop na coci yana lalata da matar wani faston da ke ƙarƙashinsa

- An dakatar da Bishop bisa laifin zina da matar malamin dake aiki a karkashin sa a Ekiti

- An dakatar da shi tsawon shekara daya kuma an umarci da ya mika komai ga Archbishop dinsa

- An kasa jin ta bakin Bishop din mai shekaru 57 har aka kammala hada rahoto saboda bai daga kiran waya

An dakatar da wani Bishop din cocin Najeriya (darikar Anglican) da ke Ekiti West, Rufus Adepoju bisa zargin sa da hannu wajen aikata badala.

Mr Adepoju, a wata wasika mai kwanan wata Disamba 11, 2020 kamar yadda Premium Times ta ruwaito, ta nuna cewa an kama shi da matar wani malamin kirista wanda ke aiki a karkashin kulawarsa.

An kama Bishop na coci yana kwanciya da matar faston da ke ƙarƙashinsa
An kama Bishop na coci yana kwanciya da matar faston da ke ƙarƙashinsa. Hoto: @Premiumtimesng
Source: Twitter

Takardar dakatarwar na dauke da sa hannun shugaban cocin Najeriya, Rev Henry Ndubuka.

Bishop din ya kuma amsa cewa ya aikata laifi.

DUBA WANNAN: 2023: Magoya bayan Tinubu sun kaddamar da yakin neman zabe

"Muna farawa da sunan Allah da Yesu Almasihu," a cikin wasikar.

"Muna rubuta wannan wasika cikin damuwa don dakatar dakai daga matsayin Bishop din Anglican Ekiti West.

"Wannan na zuwa ne biyo bayan laifin da ka aikata da kuma zina da matar malamin da yake aiki a karkashinka. An tattauna wannan abu da ya shafe ka a ranar Alhamis 10 ga Disamba 2020."

Takardar ta kuma bayyana cewa Bishop din zai shafe shekara guda ba tare da shiga al'amuran coci ba.

"Da wannan dakatarwar, ba zaka gudanar da abin da ya shafi aikin Bishop ba na tsawon shekara daya daga kwanan watan jikin wasikar, ka mika komai hannun Archbishop dinka."

"Muna addu'ar Allah ya sa kayi amfani da wannan lokacin wajen neman yafiyar ubangiji kuma zamu taya ka da addu'a. Sanya ido akan ka hakki ne na shugabannin kiristocin Najeriya. Allah ya na tare da kai."

KU KARANTA: Idan Boko Haram sun gama da Arewa, za su tunkari Kudu, Aisha Yesufu

Kokarin jin ta bakin Bishop din bai yiwu ba har zuwa lokacin da aka kammala hada wannan rahoto. Bai daga kiran wayar da aka dinga yi masa ba.

Bishop Adepoju, mai shekara 57, an nada shi bishop din Ekiti West ranar 27 ga watan Yuni 2017, bayan kusan shekara 32 yana karamim malami da kuma kusan shekara 20 yana hidima.

Shi ya maye gurbin Oludare Oke, tsohon Bishop din Ekiti West da ya ajiye aiki bayan cika shekara 70.

Da aka nemi jin ta bakin tsohon Bishop mai ritaya a ranar Talata, Bishop Oke mai ya bayyana cewa abu ne wanda ya shafi shugabancin cocin.

A wani labarin, gwamnatin tarayyar Najeriya, a ranar Lahadi ta ce shirin samar da ayyuka na musamman, SPW, guda 774,000 zai fara ne a ranar 5 ga watan Janairun shekarar 2021.

Karamin ministan Kwadago da samar da ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ne ya shaidawa The Nation hakan ranar Lahadi a Abuja.

Shirin samar da ayyukan ga masu sana'o'in hannu na watanni uku inda za a rika biyansu N20,000 duk wata ya samu tsaiko sakamakon rashin jituwa tsakanin ministan da tsohon shugaban hukumar samar da ayyuka ta kasa, NDE, Nasir Ladan da Buhari ya sallama daga aiki makon data gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel