Ina fuskantar matsin lamba akan sai na binciki gwamnatocin baya, Gwamnan Bauchi
- Gwamnn Bauchi ya bayyana cewa tarihin siyasar tsofaffin gwamnoni a Bauchi zai shafe saboda ayyukan sa
- Ya kuma bayyana cewa yana da hujjoji da zai iya bincikar tsaffin gwanoni amma aiki ne a gaban shi
- Gwamnan ya ce zai shararo aiki sosai a jihar ta yadda al'umma za su gane cewa ha'intarsu ake yi a shekarun baya
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya ce yana fuskantar matsin akan ya binciki gwamnatocin baya musamman wanda ya gada, Mohammad Abubakar, The Punch ta ruwaito.
Ya bayyana cewa tsofaffin gwamnoni za su zama tarihi a siyasar jihar saboda irin ayyukan da zai yi a jihar zuwa karshen wa'adinsa wa'adin sa.
Ya bayyana haka ne a jawabin kaddamar da aikin tituna guda hudu wanda shugaban jam'iyyar PDP na kasa Prince Uche Secandus, da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal suka kaddamar ranar Laraba a Bauchi.
DUBA WANNAN: Jerin zuri'a 5 da suka fi arziki a Najeriya
Mohammad ya ce, "mutane suna tambaya wai ina nake samun kudaden da ake ayyuka da su, akwai hanyoyi da dama a wajen gwamnati kuma akwai tarin kudi a asusun gwamnati. Abin da ke faruwa shine ba'a amfani da kudin ta hanyar da ta dace kuma mu tabbatar tsirararun mutane ba su nuna son kai ba.
"Ina da hujjoji da zan iya bincikar gwamnatocin baya amma nasan sha'anin gwamnati mai chanjawa ne
"Abin da zanyi shine aiki da dan abin da ya rage mana don mutane su yi bincike da kansu, su kuma san an ha'ince su.
KU KARANTA: 2023: Magoya bayan Tinubu sun kaddamar da yakin neman zabe
"An kai kudade wani wajen kuma zasu sha kunya kuma za a daina zancen su a siyansance don sun zuburwa kansu kima da mutunci."
Gwamnan ya kuma kara da cewa: "ayyukan da muke zai kunyata su matuka kuma zai sa a nemi jin ba'asi ko ayi bincike, amma tabbas, abin da muke bawai baiwa bace amma kudin da aka yi irin waccan ta'asar, da shi muke habbaka tattalin arziki kuma muke toshe kafar sata."
Karamin ministan Kwadago da samar da ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ne ya shaidawa The Nation hakan ranar Lahadi a Abuja.
Shirin samar da ayyukan ga masu sana'o'in hannu na watanni uku inda za a rika biyansu N20,000 duk wata ya samu tsaiko sakamakon rashin jituwa tsakanin ministan da tsohon shugaban hukumar samar da ayyuka ta kasa, NDE, Nasir Ladan da Buhari ya sallama daga aiki makon data gabata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng