Yanzu-yanzu: An zabi sabon Kakaki da mataimakinsa a majalisar dokokin Kano

Yanzu-yanzu: An zabi sabon Kakaki da mataimakinsa a majalisar dokokin Kano

- Bayan murabus din tsohon kakaki da safiyar Talata, an zabi sabi

- Yan majalisan sun zargi tsohon Kakakin da kin yaki don jin dadinsu wajen gwamnan

- Sun shekara daya kenan ba'a biya ma'aikatan majalisar alawus ba

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa an zabi Hamisu Chidari, mai wakilan mazabar Makoda a matsayin sabon Kakakin majalisar dokokin jihar Kano, TVC ta ruwaito.

Hakazalika an zabi Zubairu Musa mai wakiltan mazabar Sumaila a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar.

Labaran Madari, mai wakiltar Warawa, ya zama sabon shugaban masu rinjaye.

Yanzu-yanzu: An zabi sabon Kakaki da mataimakinsa a majalisar dokokin Kano
Yanzu-yanzu: An zabi sabon Kakaki da mataimakinsa a majalisar dokokin Kano Credit: TVC
Asali: UGC

DUBA NAN: Dalilin da ya sa muka sace dalibai a Katsina, Boko Haram

Kun ji cewa cewa tsohon kakaki majalisar Garba Gafasa ya yi murabus ne bayan samun labarin cewa 35 cikin mambobin majalisar dokokin jihar Kano 40, sun rattafa hannu domin tsigeshi da shugaban masu rinjaye ranar Talata.

Duk da cewa Kakakin da shugaban masu rinjayen basu bayyana dalilin da ya suka yi murabus ba, an tattaro cewa sun yi murabus ne gudun kada a tsige su a zaman ranar Talata.

Wani mamban majalisan ya bayyanawa Daily Nigerian cewa su biyun gwamnan kawai suke yiwa hidima ba mambobi ba.

"Mun yi fito na fito da su ne saboda sun yi kasa a gwiwa wajen jin dadinmu wajen gwamna. A watanni goma da suka gabata mambobi basu samu kudin mazabunsu ba, da kudadenmu da dama. Har alawus na ma'aikatan majalisa ba a biya ba na tsawon shekara daya," yace.

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi ya gwangwaje matashin da yayi masa tattaki daga Sokoto da motar alfarma

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel