Gwamnan Bauchi ya gwangwaje matashin da yayi masa tattaki daga Sokoto da motar alfarma
- Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya gwangwaje wani mutum da dalalleliyar mota
- Mutumin ya yi tattaki tun daga jihar Sokoto har Bauchi don nuna wa gwamnan soyayya
- Gwamnan ya yi farin ciki da tattakin, sakamakon haka ya bashi dalleliyar motar kirar Peugeot 406
Wani dan Najeriya mai suna Mustapha Yusuf ya yi tattaki tun daga jihar Sokoto har jihar Bauchi, don nunawa gwamna Bala Mohammed kauna sakamakon nasarorin da ya samu tun bayan hawansa mulki.
Gwamnan ya baiwa Yusuf kyautar mota kirar Peugeot 406 a matsayin kyauta don nuna farin cikinsa.
Mutumin ya yi tattakin ne don ya yabawa gwamnan a kan cigaban da ya samar a jiharsa, inda yake kara masa kwarin guiwa a kan ya cigaba.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace mutum 19, sun halaka fasto a Niger
Yusuf ya ce nasarorin da gwamnan ya samu suna da matukar yawa. Yayin da gwamnan yace zai tabbatar ya cigaba da dagewa wurin ciyar da jihar gaba.
Ya bashi kyautar Peugeot 406 din ne a matsayin kyautatawa da karamci. Yusuf ya nuna matukar farin cikinsa karara.
KU KARANTA: 2023: Magoya bayan Tinubu sun kai ziyarar neman goyon baya fadar babban basarake
A wani labari na daban, wani bidiyon shugaba Muhammadu Buhari ya yi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani. Bidiyon ya nuna yadda Buhari ya kaiwa shanunsa ziyara a Daura, jihar Katsina, bayan wasu sa'o'i kadan da sace daruruwan yaran makarantar GSSS Kankara.
'Yan bindiga sun sace daliban GSSS Kankara, a jihar Katsina da misalin karfe 11pm na daren Juma'a.
Bidiyon da Sahara Reporters suka wallafa a ranar Litinin, yana dauke da lokaci da kuma kwanan watan, 12 ga watan Disamban 2020, an ga Buhari da hadimansa suna zagaye wurin kiwon shanunsa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng