Dalilin da ya sa muka sace dalibai a Katsina, Boko Haram

Dalilin da ya sa muka sace dalibai a Katsina, Boko Haram

- Shugaban yan ta'adda, Shekau, ya sake ikirarin yaki don daukaka addinnin Musulunci

- Masana da Malaman addini sun karyata ikirarinsa inda suka ba haka koyarwan Musulunci take ba

- Hukumar Sojin tarayya ta dade tana neman Shekau ruwa a jallo

Kungiyar masu tada kayar bayan Boko Haram ta bayyana dalilin da yasa tayi garkuwa da daliban makarantan ilmin kimiya na kwana dake karamar hukumar Kankara, jihar Katsina.

A faifan jawabin da kungiyar ta Boko Haram ta saki a daren Litinin, 14 ga Disamba, shugabansu, Abubakar Shekau, ya yi bayanai cikin kimanin mintuna 5.

Ya ce har yanzu basu bukaci komai hannun gwamnati ba.

Humangle ta ruwaito Shekau da cewa, "Mun yi abinda ya faru a Katsina ne domin da'awar addinin Musulunci da kuma hana mutane abubuwan da suka sabawa Musulunci saboda Allah da manzonsa basu hallata Boko ba,"

"Bayan haka ba a karantar da abinda Allah da manzonsa suka karantar. Kawai suna rusa addinin Musulunci ne."

KU DUBA: Jerin sabbin Sanatocin da aka rantsar yau a majalisar dattawa

Dalilin da ya sa muka sace dalibai a Katsina, Boko Haram
Dalilin da ya sa muka sace dalibai a Katsina, Boko Haram
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi ya gwangwaje matashin da yayi masa tattaki daga Sokoto da motar alfarma

Mun kawo muku cewa Kungiyar Boko Haram ta sanar da cewa ita ce keda alhakin sace dalibai fiye da 300 daga makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara a jihar Katsina, kamar yadda HumAngle ta rawaito.

A cewar HumAngle, shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya ce har yanzu basu tuntubi kowa dangane da wasu sharuda na sakin daliban ba.

Jaridar ta ce, Shekau ya sanar da hakan ne a cikin wani sakon sautin murya mai tsawon mintuna 4:28 da ya fitar da duku-dukun safiyar ranar Talata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng