Dalilin da ya sa kakakin majalisar dokokin jihar Kano yayi murabus

Dalilin da ya sa kakakin majalisar dokokin jihar Kano yayi murabus

- An bayyana dalilin da ya sa shugabannin majalisan dokokin jihar Kano suka yi murabus

- Kakakin da shugaban masu rinjaye a majalisar sun yi murabus da safen nan

- Majalisar dokokin Kano ta yi kaurin suna da canja-canjen yan majalisa

Daily Nigerian ta ruwaito cewa 35 cikin mambobin majalisar dokokin jihar Kano 40, sun rattafa hannu domin tsige Kakakin majalisa da shugaban masu rinjaye ranar Talata.

Duk da cewa Kakakin da shugaban masu rinjayen basu bayyana dalilin da ya suka yi murabus ba, an tattaro cewa sun yi murabus ne gudun kada a tsige su a zaman ranar Talata.

Wani mamban majalisan ya bayyanawa Daily Nigerian cewa su biyun gwamnan kawai suke yiwa hidima ba mambobi ba.

"Mun yi fito na fito da su ne saboda sun yi kasa a gwiwa wajen jin dadinmu wajen gwamna. A watanni goma da suka gabata mambobi basu samu kudin mazabunsu ba, da kudadenmu da dama. Har alawus na ma'aikatan majalisa ba a biya ba na tsawon shekara daya," yace.

KU KARANTA: GSS Ƙanƙara: Masu garkuwa sun ce iyayen yara su fara tanadin kuɗin fansa, sun kuma gargadi sojoji

Dalilin da ya sa kakakin majalisar dokokin jihar Kano yayi murabus
Dalilin da ya sa kakakin majalisar dokokin jihar Kano yayi murabus Credit: https:/dailynigerian.com/kano-speaker-majority
Asali: UGC

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnatin Kaduna ta sanar da rufe dukkan makarantun jihar a karo na 2

Kun ji cewa Kakakin majalisar dokokin jihar Kano, AbdulAziz Gafasa, da wasu mutane biyu cikin shugabannin majalisan sun yi murabus daga kujerunsu.

Gafasa ya bayyana niyyarsa da magatakardan majalisan a wasikar da ya aike jiya, 14 ga Disamba, 2020.

Wani sashen jawabin yace: "Ni, Rt. Hon. Abdulaziz Garba Gafasa na sanar da kai, mambobin majalisa da jama'a gaba daya cewa na yi murabus daga matsayina na kakakin majalisa daga ranan nan bisa wasu dalilai na kaina."

"A karshe, ina godiya ga dukkan mambobin majalisan bisa goyon bayan da suka bani a lokacin da nayi matsayin Kakaki, kuma ina addu'a Allah Subhanahu wata’ala ya shiryar da sabbin shugabannin."

Wadanda suka yi murabus tare da shi, a cewar majiya, sune shugaban masu rinjaye, Kabiru Dashi, da mataimakinsa, Tasiu Zabainawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel