Kakakin majalisar dokokin jihar Kano, shugaban masu rinjaye sun yi murabus
- Shugaban majalisar dokokin jihar Kano da shugaban masu rinjaye sun yi murabus daga mukamansu
- Babu wani dalili da suka bayar na yin murabus din bayan bayyana cewa saboda wasu dalilai na kashin kai ne
- Abdulaziz Garba Gafasa, shugaban majalisar, ya sanar da cewa ya yi murabus a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 14 ga watan Disamba
Labari da dumi-duminsa da Legit.ng Hausa ta samu daga Premium Times da sanyin safiyar ranar Talata ya tabbatar da cewa shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Abdulaziz Gafasa, da wasu sauran shugabanni biyu sun yi murabus daga mukamansu.
Gafasa ya sanar da yin murabus dinsa ne a cikin wata wasika da ya mikawa magatakardar majalisar dokokin jihar Kano a ranar Litinin, 14 ga watan Disamba.
Wani bangare na wasikar na cewa, "Ni, mai girma Abdulaziz Garba Gafasa, na rubuta wannan wasika domin sanar da mambobin wannan majalisa da kuma sauran jama'a cewa na yi murabus daga mukamina na shugaban majalisar dokokin Kano saboda wasu dalilai na kaina.
KARANTA: Bamu tuntubi kowa ba; Boko Haram ta dauki nauyin sace daliban Kankara a sabon sakon Shekau
"A karshe, ina mika sakon godiya ga dukkan mambobin wannan majalisa bisa hadin kai da goyon bayan da suka bani a yayin shugabancina, ina mai addu'ar Allah Subhanahu wata'ala ya bamu sabon shugabanci nagari.
"Na ku Abdulaziz G. Gafasa."
Sai dai, Gafasa bai bayyana dalilin yin murabus dinsa ba.
KARANTA: Sakandire: Dalibai fiye da 500 sun koma makaranta dauke da juna biyu bayan hutun korona
Wata majiya daga majalisar, wacce ta bukaci a sakaya sunanta, ta sanar da Premium Times da safiyar ranar Talata, cewa Gafasa tare da wasu shugabannin majalisar biyu sun yi murabus daga mukamansu.
Ragowar shugabannin guda biyu sun hada da shugaban masu rinjaye, Kabiru Dashi, da mataimakinsa, Tasiu Zabainawa.
A kwanakin baya ne Legit.ng ta rawaito cewa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya saka hannu a kan dokar ilimi kyauta kuma dole ga dukkan yaran jihar Kano.
Kirkirar dokar ya na da nasaba da hauhawar alkaluman yaran da basa zuwa makaranta, sai gararamba da yawon bara a titunan jihar Kano.
Ganduje tsohon malamin jami'a ne a BUK kafin daga baya ya koma bangaren gudanarwa na gwamnati.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng