GSS Ƙanƙara: Masu garkuwa sun ce iyayen yara su fara tanadin kuɗin fansa, sun kuma gargadi sojoji

GSS Ƙanƙara: Masu garkuwa sun ce iyayen yara su fara tanadin kuɗin fansa, sun kuma gargadi sojoji

- Masu garkuwa da mutane da suka sace ɗaliban saknadare ta GSS Ƙanƙara a Katsina sun kira iyayen dalibi

- Sun faɗa masa ya fara tanadin kuɗin fansa sannan ya gargadi sojoji su dena 'leƙen su' idan suna son samun daliban lafiya

- Rundunar soji ta ce ba zata fasa saka ido a inda aka boye daliban ba domin abinda tasa a gaba shine ceto su lafiya

Ƴan bindigan da suka yi garkuwa da ɗaliban makarantar sakandare ta maza da ke Ƙanƙara a Katsina, sun tuntuɓi ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban.

A cewar Kadaria Ahmed, yar jarida, Abdul Labaran, kakakin gwamnatin Katsina ne ya bayyana hakan a hirar da aka yi da shi a RadioNow FM.

GSS Ƙanƙara: Masu garkuwa sun ce iyayen yara su fara tanadin kuɗin fansa
GSS Ƙanƙara: Masu garkuwa sun ce iyayen yara su fara tanadin kuɗin fansa. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Ta ce ta jiyo labaran na cewa ƴan bindigan sun faɗa wa iyaye su fara tanadin kuɗin fansa kafin a sako ɗaliban.

DUBA WANNAN: Zaben Amurka: Kwalejin zabe ta tabbatar Biden ne ya ci zabe

Labaran ya kuma ce wai ƴan bindigan sun faɗa wa iyayen ɗaliban su gargaɗi jami'an tsaro su dena musu 'leƙen asiri' a inda suka ɓoye idan ana son a samu ɗaliban lafiya.

"Abdul Labaran kakakin gwamnatin Katsina ya fadawa @RadioNow953FM cewa ƴan bindigan da suka sace ɗalibai sun kira ɗaya daga cikin iyaye sun faɗa masa ya fara tanadin kuɗin fansa ya kuma shaida wa sojoji su dena leƙen asirin inda suke ta samaniya idan kuma ba haka ba ...," Kamar yadda Kadaria ta wallafa a Twitter.

Amma a ɓangaren ta hedkwatar tsaro ta ce ba za a janye sojojin ba duk da maganar da ƴan bindigan suka yi da gwamnatin jihar.

A hirar da aka yi da shi a Channels Television a ranar Litinin, John Enenche, kakakin hedkwatar tsaro, ya ce ba za a dakatar da aikin ceto ɗaliban da sojojin ke yi ba.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Wasu da ake zargi da fashi da garkuwa sun tsere daga gidan yari

"Ba za ka dakatar da aikin ceto da sojojin ke yi ba don wata tattaunawa. Ana iya dukkan biyun a lokaci guda," in ji shi.

Ya ce idan aka kawar da kai daga inda ɗaliban suke, za su sulale da su don haka ba za a yi sakaci ba don abinda ya fi muhimmanci a yanzu shine ceto ɗaliban da lafiyarsu.

A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel