COVID-19: Gwamnatin Kaduna ta sanar da rufe dukkan makarantun jihar a karo na 2
- Gwamnatin Kaduna ta bai wa makarantu wa'adin kammala jarabawa tare da rufe azuzuwa
- Hakan ya faru ne sakamakon sabuwar guguwar cutar korona da ta tashi a jihar a karo na biyu
- Za a cigaba da koyarwa ta rediyo, talabijin da yanar gizo kamar lokacin kullen korona
Gwamnatin jihar Kaduna ta bada umarnin sake garkame makarantun jihar tare da umartarsu da su kammala jarrabawa zuwa ranar Laraba, 16 ga watan Disamban 2020.
Hakan yana zuwa ne bayan sake tasowar guguwar cutar korona a karo na biyu a fadin jihar.
A sanarwar da ma'aikatar ilimin jihar ta fitar tare da sa hannun kwamishinan ilimi, ta ce za a dakatar da dukkan koyarwa da karatu a makarantun sakandare, jami'o'i da kwalejoji da ke jihar.
An bukaci su koma karatun ta wasu hanyoyin da suka hada da rediyo, talabijin da yanar gizo.
KU KARANTA: Hotunan bikin dan Obasanjo da bidiyon motar alfarmar da ya bai wa amaryarsa
Ta kara da cewa za a koma karatun ne kamar yadda aka yi a jihar yayin kullen korona a baya.
A wani labari na daban, majalisar dattawa tana tuhumar ma'aikatar man fetur a kan bai wa wani ma'aikacinta N145,000,000, Daily Trust ta wallafa.
Korafin yana cikin wata takarda ta Odita janar na gwamnatin tarayya a 2015, wacce kwamitin majalisar dattawa na asusun gwamnati ta amsa.
Kwamitin, wanda Sanata Matthew Urhoghide yake shugabanta, ta yi bincike a kan kudaden da ma'aikatun gwamnatin tarayya suke kashewa.
Kamar yadda takardar tazo: "MTB ta amince da bayar da N145,000,000, kuma ta biya wani ma'aikacinta don tallace-tallace na gidajen talabijin da jaridu na tallar PIB, maimakon a bai wa kwararrun kuma masana harkar damar baje gwanintarsu don a tabbatar da wanda ya cancanci kwangilar."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng