Yanzu-yanzu: Antoni Janar na Amurka Bill Barr ya yi murabus

Yanzu-yanzu: Antoni Janar na Amurka Bill Barr ya yi murabus

- Antoni Janar na kasar Amurka Bill Barr ya ajiye aikinsa

- Shugaban Amurka Donald Trump ne ya sanar da haka a shafinsa na Twitter

- Trump ya ce dangantakarsa da Barr mai kyau ne amma zai tafi daf da Kirsimeti

Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Litinin ya ce Antoni Janar Bill Barr, wadda ya ki amincewa da ikirarin da ya yi na cewa an tafka magudi a zaben shugaban kasa na ranar 3 ga watan Nuwamba zai ajiye aiki bayan yin 'aiki nagari.'

"Yanzu muka gama ganawa da Antoni Janar Bill Barr a White House," kamar yadda Trump ya wallafa a Twitter. "Dangartakar mu ta kasance mai kyau ne ... Bill zai bar mu daf da Kirsimeti don yin hutu tare da iyalansa."

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Wasu da ake zargi da fashi da garkuwa sun tsere daga gidan yari

Yanzu-yanzu: Antoni Janar na Amurka Bill Barr ya yi murabus
Yanzu-yanzu: Antoni Janar na Amurka Bill Barr ya yi murabus
Source: Original

KU KARANTA: FG ta sanar da ranar da ma'aikata 774,000 za su fara aiki

Trump ya kuma sanar da cewa mataimakin Antoni Jeff Rosen zai kama aiki a matsayin Antoni Janar na wucin gari yayin da Richard Donoghue zai maye gurbin mataimakin Antoni Janar.

"Mataimakin Antoni Janar Jeff Rosen zai sama mataimakin Antoni Janar na rikon kwarya yayin da Rochar Donoghue zai maye gurbin mataimakin Antoni Janar. Nagode."

A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel