Karya ne, ba kashesu akayi ba, hadari suka yi: Gwamnatin Kaduna kan mutuwan yan Kano 16 (Hotuna)

Karya ne, ba kashesu akayi ba, hadari suka yi: Gwamnatin Kaduna kan mutuwan yan Kano 16 (Hotuna)

- Gwamnatin Kaduna da hukumar yan sanda sun yi fashin fashi kan mutuwar yan jihar Kano 16

- An yi rashin rayukan akalla matafiya 16 yayinda suka nufi Kano daga Abuja

- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya yi Alla-wadai da wannan abu

Gwamnatin jihar Kaduna ta karyata rahotanni da jawabin gwamnatin jihar Kano cewa yan bindiga sun hallaka yan Danbatta 16 a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kwamishanan tsaro da harkokin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa hadari sukayi, ba yan bindiga suka kashesu ba.

Hakazalika ya ce hadarin ya faru ne tsakanin Kaduna da Zariya ba tsakanin Kaduna da Abuja ba kamar yadda sakataren yada labaran gwamnatin Kano ya fadi.

"Labarin cewa yan bindiga sun kashe yan asalin jihar Kano 16 a hanyar Kaduna zuwa abuja karya ne kuma ba daidai bane, " Aruwan yace.

"Gaskiyar magana itace sun mutu ne a Rigachikun, hanyar Kaduna zuwa Zariya sakamakon hadarin mota bayan tayarsu ta fashe."

"Muna jajantawa iyalansu, kuma muna addu'a Allah ya jikansu. Hakazalika muna yiwa wadanda suka jikkata fatan samun lafiya."

KU DUBA: Hatsarin mota ya halaka mutane 40 a Adamawa, FRSC

Karya ne, ba kashesu akayi ba, hadari suka yi: Gwamnatin Kaduna kan mutuwan yan Kano 16 (Hotuna)
Karya ne, ba kashesu akayi ba, hadari suka yi: Gwamnatin Kaduna kan mutuwan yan Kano 16 (Hotuna)
Source: Depositphotos

Hakazalika kwamishanan yan sanda jihar, Umar Muri, ya saki jawabin cewa motar ta kwacewa direban a daidai Rigachikun kuma motar ta juya inda mutane 9 suka rasa rayukansu kai tsaye.

Yace sauran mutane 9 dake cikin motan sun jikkata kuma na kaisu asibiti a unguwar Kakuri.

Ya ce bakwai cikin wadanda aka kai asibitin sun kwanta dama, yayinda sauran uku na jinya yanzu.

DUBA NAN: Lai, Gbemisola da Abdulrazaq su na yakin karbe Jam’iyyar APC a Jihar Kwara

A jiya mun kawo muku cewa yan bindiga sun yi sanadiyar mutuwar mutane 16 yan asalin jihar Kano a kan hanyar su ta dawowa kano daga Abuja a babban titin Kaduna zuwa Abuja.

Wata majiya daga karamar hukumar Danbatta ta tabbatar da cewa mutanen yan asalin karamar hukumar sun gamu da ajalinsu bayan da yan bindiga suka harbi tayar bus din da suke ciki.

Gwamnatin jihar ta jajantawa iyalan mamatan tare da bayyana bakin ciki da bacin rai tare da jajantawa yan karamar hukumar Danbatta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel