Hatsarin mota ya halaka mutane 40 a Adamawa, FRSC

Hatsarin mota ya halaka mutane 40 a Adamawa, FRSC

- Hukumar FRSC reshen Jihar Adamawa ta ce a ƙalla mutum 40 ne hatsarin mota ya kashe a jihar daga Satumba zuwa 9 ga Disamba

- Kwamandan hukumar ya ce abubuwan da suka fi janyo hatsarin sun hada da gudu fiye da kima, obatekin ba bisa ka'ida ba da sauransu

- Hukumar ta bawa masu ababen hawa shawarwarin yadda za su kare kansu musamman a karshen shekara da akafi samun hatsari

Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta Kasa, FRSC, reshen jihar Adamawa ta ce a ƙalla mutane 40 ne suka rasu sakamakon hatsarin mota daga watan Satumba zuwa 9 ga watan Disamba.

Hukumar ta kuma ce mutum 203 sun samu mabanbantan raunuka, Vanguard ta ruwaito.

Mista Ocheja Ameh, kwamandan FRSC na Adamawa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai, NAN, a ranar Juma'a a Yola cewa an kuma samu hatsarin mota 82 daga Satumba zuwa 9 ga watan Disamba.

Hatsarin mota ya halaka mutane 40 a Adamawa, FRSC
Hatsarin mota ya halaka mutane 40 a Adamawa, FRSC. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yan sanda sun ce sun kashe kasurgumin dan bindiga a Niger

Ya ce hatsarin ya ritsa da motocci 138 da mutane 407 cikinsu inda hukumar tayi nasarar ceto 364 ta kai su asibitoci mafi kusa.

Ya ce abubuwan da suka fi sanadin hatsarin sun hada da gudu fiye da kima, tayoyi marasa kyau, obatekin ba bisa ka'ida ba da ƙwacewa da motocci ke yi wa direbobi.

Kwamandan ya yi kira ga masu ababen hawa su kula da dokokin tuki su kuma dinga mutunta ma'aikatan da ke kula da dokokin hanya.

KU KARANTA: Tambuwal zai kirkiri Hisbah a jihar Sokoto

Ya kuma gargadi amfani da wayar salula yayin tuki musamman a yanzu da ake samun ƙaruwar hatsari.

"Mun iso lokacin da aka fi samun hatsari, kuyi tuki cikin tsanaki, ku dinga duba tayoyin ku sannan ku guji ɗaukan kayan da yafi ƙarfin mota don zamu sa ido kan hakan", in ji shi.

Daga ƙarshe ya ce, baza jami'an hukumar zuwa ƙananan hukumomi 21 na jihar ya taimaka wurin wayar da kan mutane.

A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.

The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.

Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel