2023: PDP ta magantu a kan bai wa Jonathan tikitin takarar shugaban kasa
- Shugaban jam'iyyar PDP na kasa ya ce Jonathan zai iya fafutukar neman tikitin tsayawa takara a 2023 karkashin jam'iyyar
- A cewarsa, kin amsa gayyatar majalisar tarayya da Buhari yayi, alama ce da ke nuna yayi burus da 'yan Najeriya
- Ya kara da cewa, masu guduwa daga jam'iyyar PDP zuwa APC suna saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya
Prince Uche Secondus, Shugaban jam'iyyar PDP na Najeriya ya ce Jonathan zai iya fafutukar neman tikitin tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar.
Sauran jiga-jigan jam'iyyar masu ra'ayin tsayawa takarar za su iya yakin neman tikitin, kamar yadda shugaban jam'iyyar yace, The Nation ta wallafa.
Secondus ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari a kan kin amsa gayyatar majalisar tarayya, wacce ta bukaci yayi magana a kan matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar nan.
KU KARANTA: Buhari ya sanar da gwamnoni hanyar da za su bi wurin magance rashin tsaro
A cewarsa, rashin amsa gayyatar majalisar kamar share gaba daya mutanen Najeriya ne, saboda su suka zaba a matsayin wakilansu.
Secondus ya ce rashin amsa gayyatar tasa alama ce da take nuna cewa ba shi da wani abu da zai fadi a kan kokarin gyara harkokin rashin tsaron da ke kasar nan.
A cewarsa, "Wannan kame-kamen da shugaban kasa yake yi alama ce wacce take nuna cewa ya gaza a shugabancinsa.
"Yin burus da wakilan jama'a kamar share gaba daya 'yan Najeriya ne. A gaskiya, hankula a tashe suke, shugaban kasa bai damu da damuwarmu ba, idan ba haka ba mai zai sa ya kasa fuskantar jama'a yayi musu bayani?
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace basarake, sun hada da mutum 12 a Katsina
"Babbar matsalar mu a yanzu shine yadda gaba daya Najeriya ta lalace, kuma gwamnati bata da niyyar yin komai a kai."
Ya kara da cewa duk wadanda aka zaba a karkashin jam'iyyar PDP suka koma jam'iyyar APC sun aikata abinda bai dace ba. Sannan yakamata majalisar tarayya dauki mataki a kansu, saboda hakan ya saba wa doka.
A cewarsa, "Ba na tunanin shugabannin majalisar tarayya suna amfani da kundin tsarin mulkin kasar nan. Idan da suna yi, da basu bari ana wannan canje-canjen jam'iyyar ba."
A wani labari na daban, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce 'yan majalisar dattawa ba kansu suke yi wa aiki ba, jaridar The Cable ta wallafa.
Yayin da Lawan yake jawabi a wani taro a majalisar ranar Laraba, ya ce 'yan majalisar dattawa suna sane da abubuwan da suke yi.
A cewarsa, 'yan majalisar sune wadanda suka fi saukin zuwa garesu cikin wadanda aka zaba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng