Lawan: 'Yan majalisar dattawa ba kansu suke wa aiki ba, Ahmad Lawan

Lawan: 'Yan majalisar dattawa ba kansu suke wa aiki ba, Ahmad Lawan

- Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce suna iyakar kokarinsu

- A cewarsa kullum cikin zarginsu ake yi da gyara aljihunsu kuma a gaskiya ba hakan bane

- Ya ce sun fi duk wasu ma'aikatan gwamnati taka tsan-tsan, kuma suna bukatar addu'a

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce 'yan majalisar dattawa ba kansu suke yi wa aiki ba, jaridar The Cable ta wallafa.

Yayin da Lawan yake jawabi a wani taro a majalisar ranar Laraba, ya ce 'yan majalisar dattawa suna sane da abubuwan da suke yi.

A cewarsa, 'yan majalisar sune wadanda suka fi saukin zuwa garesu cikin wadanda aka zaba.

Lawan: 'Yan majalisar dattawa ba kansu suke wa aiki ba, Ahmad Lawan
Lawan: 'Yan majalisar dattawa ba kansu suke wa aiki ba, Ahmad Lawan. Hoto daga @Thecableng
Asali: Facebook

KU KARANTA: Hotuna: Direba ya ragargaza kan jami'in LASTMA da tabarya, ya bar shi rai a hannun Allah

"Wajibi ne a yi zaben gaskiya da gaskiya a 2023, kuma dole mu mayar da hankali. Idan kun gano wani abu wanda ya dace a yi, ku taimaka ku sanar damu. Kada ku dinga jira mu yi kuskure, sai ku fara fallasawa, kuna cewa wadannan aljihunsu kawai suke gyarawa.

"Daga dan zamana, na fahimci cewa 'yan majalisar nan ba kansu suke yi wa aiki ba. Kuma wannan majalisar tana daya daga cikin wuraren da suka fi taka tsan-tsan.

"Duk abinda za mu yi sai mun bayyana shi, sannan an fi samun damar zuwa wurinmu," yace.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta sanar da lokacin bayyana yankin da za ta ba wa tikitin takarar shugaban kasa

Ya ce za a yi gyara a kan kundin tsarin mulki kafin watanni 3 na farkon shekarar 2021 su wuce.

"Mutane za su iya sukarmu, ko kuma zarginmu da yin yadda muka ga dama. Amma muna yin iyakar kokarinmu" yace.

A wani labari na daban, a taron da shugaba Buhari yayi da gwamnoni, ya zauna tsaf ya saurari korafi daga yankuna 6 da ke kasar nan, daga bakin gwamnoni, a kan harkokin tsaro da ke addabar kasarnan.

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Garba Shehu yace, shugaban kasa ya ce, "Wajibi ne gwamnati tayi aiki tare da shugabannin gargajiya. Ya kamata a hada kai dasu don a san ta inda za a bullo wa lamarin."

Buhari ya ce mulkinsa ya yi kokarin gyara yankunan arewa maso gabas da kudu-kudu, amma yankin kudu-kudu suna cikin mawuyacin hali, Daily Trust ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng