Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace basarake, sun hada da mutum 12 a Katsina

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace basarake, sun hada da mutum 12 a Katsina

- 'Yan bindiga sun kara kai farmaki karamar hukumar Sabuwa da ke jihar Katsina

- Sun yi garkuwa da fiye da mutane 13 a kauyen Gamji, ciki har da dagacin kauyen

- Wani ganau ya shaida yadda 'yan ta'addan suka zarce sa'o'i 3 suna barna ba tare da jami'an tsaro sun kai dauki ba

'Yan bindiga sun yi garkuwa da fiye da mutane 13 a kauyen Gamji da ke karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina, ciki har da dagacin kauyen, Malam Falalu Galadima.

Katsina Post sun bayyana yadda 'yan ta'adda suka je kauyen da misalin 1:30am na ranar Laraba.

A cikin wadanda aka yi garkuwa dasu har da wani dalibin shari'a da ke karatu a jami'ar Yenagoa, mai suna Mahdi Abdussalam.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace basarake, sun hada da mutum 12 a Katsina
Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace basarake, sun hada da mutum 12 a Katsina. Hoto daga @daily_trust
Source: UGC

KU KARANTA: Rashin tsaro: Abinda gwamnoni suka sanar da Buhari, Adesina

Sannan 'yan bindigan sun kai hari Unguwar Mato da wani kauye a karamar hukumar Faskari da ke jihar.

Wani ganau, ya bayyana yadda 'yan ta'addan suka kai kusan sa'o'i 3 suna ta'addanci ba tare da jami'an tsaro sun kai dauki ba.

Duk da dai rundunar sojin sama ta Operation Sahel Sanity suna iyakar kokarinsu wurin dakatar da 'yan ta'adda a yankin Katsina da jihar Zamfara.

KU KARANTA: Hotuna: Direba ya ragargaza kan jami'in LASTMA da tabarya, ya bar shi rai a hannun Allah

A wani labari na daban, jam'iyyar APC ce take da alhakin tsayar da dan takarar shugabancin kasa na watan Yunin 2023, kamar yadda majiya daga jam'iyyar ta tabbatar wa da Daily Trust a ranar Talata.

Majiyar ta ce idan har a arewa ta fitar da shugaban jam'iyya, kudu za a baiwa damar fitar da dan takarar shugaban kasa, ko kuma arewa ta fitar da dan takarar shugaban kasa, kudu ta fitar da shugaban jam'iyya.

A taron gaggawa da NEC tayi, ta kara wa Mai Mala Buni wa'adin cigaba da shugabancin kwamitin rikon kwaryar na watanni 6. Dama wa'adin shugabancinsa na kwamitin zai kare ne a ranar 25 ga watan Disamba, amma NEC ta kara wa'adin zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2021.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel