Buhari ya sanar da gwamnoni hanyar da za su bi wurin magance rashin tsaro
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnoni su yi aiki da shugabannin gargajiya
- A cewarsa, aiki dasu ne kadai zai bai wa gwamnati damar sanin halin da al'umma take ciki, da labarai a kan 'yan ta'adda
- Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a wani taro da yayi da gwamnonin jihohi 36, inda suka tattauna a kan halin da kasa take ciki
A taron da shugaba Buhari yayi da gwamnoni, ya zauna tsaf ya saurari korafi daga yankuna 6 da ke kasar nan, daga bakin gwamnoni, a kan harkokin tsaro da ke addabar kasarnan.
Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Garba Shehu yace, shugaban kasa ya ce, "Wajibi ne gwamnati tayi aiki tare da shugabannin gargajiya. Ya kamata a hada kai dasu don a san ta inda za a bullo wa lamarin."
Buhari ya ce mulkinsa ya yi kokarin gyara yankunan arewa maso gabas da kudu-kudu, amma yankin kudu-kudu suna cikin mawuyacin hali, Daily Trust ta wallafa.
KU KARANTA: Budurwa ta banka wa saurayinta wuta saboda ya ki aurenta (Hotuna)
"Kullum ina samun labarin wata baraka da kuma fasa bututun man fetur. Ya kamata a dakatar da satar mai," inji Buhari.
Yayin da shugaban kasa yake magana a kan al'amarin ta'addanci da garkuwa da mutane a kowanne yanki, ya ce wajibi ne a tabbatar an kare kasa daga ta'addanci.
"Za mu tabbatar sojoji sun kawo karshen duk wasu 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane."
Ya ce dalilin rufe iyakar kasa duk don a kiyaye shigowa da miyagun makamai da kwayoyi ne.
"Amma yanzu haka muna son mu bude iyakokin kasar nan kusa," a cewarsa.
Shugaba Buhari ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa za su yi iyakar kokarinsu wurin ganin karshen ta'addanci a kasar nan.
KU KARANTA: Bayan kama budurwarsa tana cin amanarsa, saurayi ya bukaci shawara a kan abinda ya dace da ita
A wani labari na daban, Femi Adesina, mai ba wa shugaban kasa shawara na musamman a kan yada labarai, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar wa gwamnonin jihohi 36 cewa mulkinsa ya zage damtse wurin kawo karshen rashin tsaro a kasar nan.
A wani taro da aka yi a ranar Talata, 8 ga watan Disamba, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum da takwarorinsa na jihohin arewa maso gabas basu tayar da zancen kawo wasu mayaka ba don kawar da 'yan ta'addan Boko Haram a yankinsu.
The Punch ta ruwaito yadda Zulum ya bayyana bukatunsa 6 ga gwamnatin tarayya don kawo karshen ta'addancin 'yan Boko Haram bayan kashe manoman shinkafa 43 da suka yi a Borno, watan da ya gabata.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng