Ina mutanen suke ne? Ma'aikatan INEC na diban minshari saboda an kauracewa zabe

Ina mutanen suke ne? Ma'aikatan INEC na diban minshari saboda an kauracewa zabe

- Mutane sun tafi harkokin gabansu duk da dokar hana sufurin motoci a wuraren da ake zabe

- Wadanda ke zaune a gida kuwa sun yi amfani da hakan wajen hutawa da iyalansu

- Mafi akasari sun ki fitowa zaben cike gurbin kujerun yan majalisu

Ma'aikatan hukumar gudanar da zaben kasa, INEC, na diban minsharinsu ranar Asabar a Ikorodu yayinda mutane suka ki fitowa zaben maye cike gibin kujeran sanata mai wakiltar Legas ta gabas.

Yawancin matasan masu matsakaicin shekaru da suka yi zanga-zangan EndSARS sun ki fitowa kada kuri'unsu.

Saboda haka, jami'an INEC suka dukufa suna baccinsu.

Ina mutanen suke ne? Ma'aikatan INEC na diban minshari saboda an kauracewa zabe.

KU DUBA: Jami'an EFCC sun damke hadimin Gwamnan Bauchi da makudan kudi yana sayen kuri'u

Ina mutanen suke ne? Ma'aikatan INEC na diban minshari saboda an kauracewa zabe
Ina mutanen suke ne? Ma'aikatan INEC na diban minshari saboda an kauracewa zabe Hoto: www.pmnewsnigeria.com
Source: UGC

A bangare guda, mutane sun kauracewa zaben cike gibin kujeran Sanatan Legas ta gabas da mazabar Kosofe a dukkan kananan hukumomi biyar dake karkashin mazabar.

Akalla mutane 1,343,448 da suka yi rijista ake kyautata zaton zasu fito zabe a rumfuna 1,978 dake mazabar.

An bude rumfunan zaben misalin karfe 9 na safe amma mutane sun ki fitowa kada kuri'unsu.

Yayinda ma'aikatan hukumar zabe ke zaune domin gudanar da abubuwa, mutane yan kalilan aka gani a rumfunan.

KU DUBA: APC vs PDP: Jerin yan takaran dake karawa a zabukan maye gibi yau Asabar, 5 ga Disamba

Hakazalika a jihar Plateau, mutane sun kauracewa zaben cike gibin Sanata Longjam da ya mutu.

Daily Trust ta gano cewa a garin Yelwa, karamar hukumar Shendam, ma'aikatan INEC sun bude rumfunan zabe amma mutane sun ki fitowa yayinda wasu suka tafi harkokin gabansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel