Jama'a sun kauracewa zaben ciki gibi a Legas da Plateau

Jama'a sun kauracewa zaben ciki gibi a Legas da Plateau

Mutane sun kauracewa zaben cike gibin kujeran Sanatan Legas ta gabas da mazabar Kosofe a dukkan kananan hukumomi biyar dake karkashin mazabar.

Akalla mutane 1,343,448 da suka yi rijista ake kyautata zaton zasu fito zabe a rumfuna 1,978 dake mazabar.

An bude rumfunan zaben misalin karfe 9 na safe amma mutane sun ki fitowa kada kuri'unsu, wakilin Daily Trust ya shaida.

Yayinda ma'aikatan hukumar zabe ke zaune domin gudanar da abubuwa, mutane yan kalilan aka gani a rumfunan.

Daily Trust ta kara da cewa misali a rumfar zabe ta 48 a gunduma ta shida, an bude rumfar zabe misalin karfe 9 amma mutane biyu kadai aka gani a wajen.

Plateau

Hakazalika a jihar Plateau, mutane sun kauracewa zaben cike gibin Sanata Longjam da ya mutu.

Daily Trust ta gano cewa a garin Yelwa, karamar hukumar Shendam, ma'aikatan INEC sun bude rumfunan zabe amma mutane sun ki fitowa yayinda wasu suka tafi harkokin gabansu.

Misalin karfe 9 an safe, babu wanda aka gani yana niyyar kada kuri'a.

KU KARANTA: Jami'an EFCC sun damke hadimin Gwamnan Bauchi da makudan kudi yana sayen kuri'u

Jama'a sun kauracewa zaben ciki gibi a Legas da Plateau
Jama'a sun kauracewa zaben ciki gibi a Legas da Plateau Credit: @daily_trust
Asali: Twitter

KU DUBA: Ina mutanen suke ne? Ma'aikatan INEC na diban minshari saboda an kauracewa zabe

Mun kawo muku cewa bayan an dage zabukan har sau biyu sakamakon annobar cutar Korona da zanga-zangan EndSARS, hukumar gudanar da zaben kasa INEC zata gudanar da zabukan maye gibi 15 a yau Asabar.

Yayinda shida ciki na kujeran Sanatoci ne, tara na kujerun yan majalisan dokokin jiha ne. Akalla yan takara 143 wanda ya kunshi maza 127 da mata 16 ne zasu kara a zabukan yau.

Jihohin da za'a yi wadannan zabuka sune Bayelsa, Borno, Bauchi, Cross River, Enugu, Imo, Kogi, Katsina, Lagos, Nasarawa, Plateau da Zamfara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel