Da duminsa: Jami'an EFCC sun damke hadimin Gwamnan Bauchi da makudan kudi yana sayen kuri'u

Da duminsa: Jami'an EFCC sun damke hadimin Gwamnan Bauchi da makudan kudi yana sayen kuri'u

- Jami'an EFCC sun cika hannu da wani babban jigon jam'iyyar PDP a Bauchi

- Ana zarginsa da aikata laifin ba cin hanci da rashawa yayi zabe

- An mika shi ga yan sanda kuma sun yi awon gaba shi

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta damke Abdon Dalla, babban mai baiwa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, shawara kan harkokin kwadago.

An damke Abdon Dalla ne da makudan kudade ana zargin yana sayen kuri'u.

Jami'an sun yi awon gaba da Dalla ne ranar Asabar yayin zaben maye gibin kujerar majalisar dokokin mazabar Dass.

An ruwaito Jami'an EFCC sun damkeshi da kudi N1.5m cikin motarsa, kuma aka mikashi ga yan sanda domin bincike.

Shugaban karamar hukumar Dass. Suleiman Mohammed, ya bayyanawa manema labarai cewa kudin da aka kama a hannunsa na ma'aikatan zaben jam'iyyar PDP ne ba nashi ba.

Shugaban, ya ce an damke Dalla ne kawai bayan ya yi jawabi ga yan jarida bayan zabe.

"Na samu labarin an damke daya daga cikin mutanenmu kuma na zo domin taya shi jaje. Ban yi magana da shi ba amma na samu labarin cewa an damkeshi ne bayan jawabin da ya yiwa yan jaridar," Jaridar Guardian ta ruwaito shugaban da cewa.

"Kudin ba nashi bane, kudin ma'aikatan zaben jam'iyyarmu ne."

KU KARANTA: Zaben maye gurbi: 'Yan bindiga sun tarwatsa masu kada kuri'a a Zamfara

Da duminsa: Jami'an EFCC sun damke hadimin Gwamnan Bauchi da makudan kudi yana sayen kuri'u
Da duminsa: Jami'an EFCC sun damke hadimin Gwamnan Bauchi da makudan kudi yana sayen kuri'u
Asali: UGC

KU KARANTA: Jama'a sun kauracewa zaben ciki gibi a Legas da Plateau

Bayan an dage zabukan har sau biyu sakamakon annobar cutar Korona da zanga-zangan EndSARS, hukumar gudanar da zaben kasa INEC zata gudanar da zabukan maye gibi 15 a yau Asabar.

Yayinda shida ciki na kujeran Sanatoci ne, tara na kujerun yan majalisan dokokin jiha ne.

Akalla yan takara 143 wanda ya kunshi maza 127 da mata 16 ne zasu kara a zabukan yau.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel