Zabukan mayen gibi: Yan takara 143 da zasu kara a jihohi 11 yau

Zabukan mayen gibi: Yan takara 143 da zasu kara a jihohi 11 yau

Bayan an dage zabukan har sau biyu sakamakon annobar cutar Korona da zanga-zangan EndSARS, hukumar gudanar da zaben kasa INEC zata gudanar da zabukan maye gibi 15 a yau Asabar.

Yayinda shida ciki na kujeran Sanatoci ne, tara na kujerun yan majalisan dokokin jiha ne.

Akalla yan takara 143 wanda ya kunshi maza 127 da mata 16 ne zasu kara a zabukan yau.

Jihohin da za'a yi wadannan zabuka sune Bayelsa, Borno, Bauchi, Cross River, Enugu, Imo, Kogi, Katsina, Lagos, Nasarawa, Plateau da Zamfara.

Cikin wadannan Jihohi, Bayelsa ce mafi yawa inda za'a yi na kujerar Sanata biyu; Bayelsa ta tsakiya da Bayelsa ta yamma.

A Bayelsa ta tsakiya, mutane da suka rijista 418,109 zasu zabi mutum daya cikin mutane 11. A Bayelsa ta yamma kuwa, yan takara 14 ne mutane 234, 469 zasu zabi daya.

Sauran zabukna kujerin Sanata sune a Imo ta Arewa (Yan takara 14), Legas ta gabas (Yan takara takwas), Cross River ta Arewa (Yan takara 9) da Plateau ta kudu (Yan takara 10)

Kujerun kananan hukumomin 11 da ake kan yi yanzu haka suna mazabar mazabar Bakori (Katsina), mazabar Bakura (Zamfara), mazabar Bayo (Borno), mazabar Ibaji (Kogi), mazabar Isi-Uzo (Enugu), mazabar Kosofe (Lagos), mazabar Nganzai (Borno), Obudu (Cross River).

KU KARANTA: Karya ne, bamu baiwa Ganduje Farfesa ba, jami'ar East Carolina

Zabukan mayen gibi: Yan takara 143 da zasu kara a jihohi 11 yau
Zabukan mayen gibi: Yan takara 143 da zasu kara a jihohi 11 yau
Source: Instagram

KU KARANTA: Idan iyayenka sun haifeka dan Halas, ka shigo Zamfara kai kadai: Matawalle ga Yari

Mun kawo muku cewa majalisar dattawa a ranar Talata ta tabbatar da nadin Farfesa Mahmood Yakubu, a matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa INEC na karin shekaru biyar.

Tabbatar da shi ya biyo bayan rahoton da kwamitin majalisar dattawa kan INEC karkashin jagorancin Sanata Kabiru Gaya, ta gabatar a zauren majalisa kuma aka bukaci a amince da shi.

Sanatocin sun siffanta Farfesa Yakubu a matsayin wanda ya cancanci cigaba da zama shugaban hukumar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel