Zaben maye gurbi: 'Yan bindiga sun tarwatsa masu kada kuri'a a Zamfara

Zaben maye gurbi: 'Yan bindiga sun tarwatsa masu kada kuri'a a Zamfara

- Ana dab da fara zaben maye gurbi a karamar hukumar Bakura, 'yan bindiga sun tarwatsa jama'a

- Wurin 8:30 na safe, 'yan ta'addan sun bayyana daga dajin da ke kusa inda suka kai wa jama'a hari

- Babu kakkautawa jami'an tsaro suka shawo kan ala'amarin sannan jama'a suka dawo

Wasu mutane dauke da makamai da ake zargin 'yan bindiga ne sun tarwatsa masu kada kuri'a a kauyen Oroji da ke gundumar Rini ta karamar hukumar Bakura da ke jihar Zamfara a ranar Asabar.

Lamarin ya faru a ranar Asabar yayin da ake zaben maye gurbi na majalisar dattawa, kamar yadda rahoto daga HumAngle ya bayyana.

Jaridar Daily Trust ta bayyana yadda wani mai kada kuri'a mai suna Sulaiman Muhammad, yake sanar da cewa lamarin ya faru wurin karfe 8:30 na safe yayin da ake dab da fara saka kuri'u.

Zaben maye gurbi: 'Yan bindiga sun tarwatsa masu kada kuri'a a Zamfara
Zaben maye gurbi: 'Yan bindiga sun tarwatsa masu kada kuri'a a Zamfara. Hoto daga @HumAngle
Asali: Twitter

KU KARANTA: Babban laifi ne cigaba da ajiye hafsoshin tsaro, Shekarau ya kalubalanci Buhari

"Ma'aikatan zaben na isowa aka fara shirin saka kuri'u amma sai ga wasu 'yan bindiga daga daji sun bayyana sannan suka tarwatsa wurin," Muhammad yace.

"Daga jami'an hukumar har masu saka kuri'u sun tsere amma jami'an tsaro sun bi ta kan 'yan bindigar," yace.

A rumfar zabe mai lamba 008, Shiyyar Galadima da ke kauyen Rini, jami'an tsaron sun dinga harbi a cikin iska domin dawo da zaman lafiya bayan 'yan bindigan sun tarwatsa jama'a.

Hakazalika, rikici ya barke bayan da kwamishinan kananan hukumomi da al'amuran masarautu, Alhaji Yahaya Gora, tsohon kwamishina Alahji Muttaka Rini da kuma mataimakiyar shugaban jam'iyyar PDP, hajiya A'i Maradun sun isa rumfar zabe.

KU KARANTA: Gagarumin rikici ya barke bayan 'yan daba sun fada kotu tare da fatattakar alkali da lauyoyi

Bayan jami'an tsaron sun fatattaki 'yan bindigan, an cigaba da zabe kamar yadda rahotanni suka nuna.

A wani labari na daban, Ishaku Elisha Abbo, Sanata mai wakiltar mazabar Adamawa ta arewa ya tsallake rijiya da baya.

Kamar yadda Legit.ng ta ga wata takarda wacce tazo daga ofishin yada labaran sanatan, wani mutum mai dauke da bindigar toka ya lallabo ya tare shi, inda yayi barazanar harbinsa matsawar bai bashi miliyan 2 ba.

Takardar, wacce hadimin sanatan a kan harkokin yada labarai, Michael Volgent ya saka hannu, ya ce al'amarin ya faru ne da misalin 2pm, inda matasa da yawa suka tare hanyar, yana hanyarsa ta zuwa bikin dan uwansa da ke Mubi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel