Kin sallaman Buratai da takwarorinsa, Buhari na karya doka: Malam Ibrahim Shekarau

Kin sallaman Buratai da takwarorinsa, Buhari na karya doka: Malam Ibrahim Shekarau

- Yan majalisar dattawan Najeriya sun bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sallami hafsoshin tsaro

- Tsohon gwamnan jihar Kano ya jaddada wannan bukata na yan majalisan

- Ya ce ko ba dan rashin kokari ba, bai kamata a cigaba da ajiye hafsoshin tsaron ba

Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari na karya doka idan ya cigaba da tuburewa kan kin sallaman hafsoshin tsaron Najeriya.

Sakamakon kisan manoma a Zabarmari na jihar Borno, yan Najeriya sun jaddada kira ga sauke hafsoshin tsaro saboda wadanda ke kai yanzu sun gaza.

Shekarau wanda yayi magana a shirin Sunrise Daily na tashar Channels, ya ce ban da maganan gazawarsu, Sojoji sun zarce shekarun da ya kamata suyi, kuma ana saba doka idan suka cigaba da zama.

"Shugaban kasa na karya doka, doka ta ce idan mutum ya kai shekara 60 ya tafi, haka yake," Yace.

"Idan ka kai shekaru 35 a ofis, wajibi ne ka tafi. Kai, ba ma'aikatan shugaban kasa bane, ma'aikatan gwamnatin Najeriya ne kuma akwai doka."

Tsohon gwamnan jihar Kanon ya ce shi a ra'ayinsa kawai a bi doka kuma wajibi ne fadar shugaban kasa ta dau mataki.

Shekarau yace cikin dukkansu, babu wanda wa'adinsa bai kare ba ko ya kai shekara 60 ba.

KU KARANTA: Lauyan Maina ya yi watsi da shi, ya janye daga kareshi a kotu

Kin sallaman Buratai da takwarorinsa, Buhari na karya doka: Malam Ibrahim Shekarau
Kin sallaman Buratai da takwarorinsa, Buhari na karya doka: Malam Ibrahim Shekarau
Source: Twitter

KU KARANTA: Majalisar dattawa ta tabbatar da Farfesa Mahmood Yakubu matsayin shugaban INEC

Mun kawo muku cewa majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sallami hafsoshin tsaro da suka dade kan mulki.

Yan majalisan sun yanke wannan shawara na aikewa Buhari sakon ne sakamakon kudirin da Sanata mai wakiltar Borno ta tsakiya, Kashim Shettima, ya gabatar gaban majalisa.

Hafsoshin tsaron da ya kamata a ce tuni sun yi ritaya amma shugaba Buhari ke cigaba da amfani sune shugabansu, Janar Gabriel Olonisakin; shugaban sojin kasa, Laftanan Janar Tukur Buratai; Shugaban Mayakan Sama, Air Marshal Sadique Abubakar da shugaba Sojin ruwa, Ibok-Ete Ekwe Ibas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Kalli bidiyon jawabinsa:

Source: Legit.ng

Online view pixel