Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta bukaci Buhari ya sallami Buratai, Sadiqu Baba, dss
- Bayan kisan gillan da aka yiwa manoma 43 a Borno, mambobin majalisar dokoki sun fusata
- Sanatocin sun gabatarwa Buhari bukati akalla 9 na abubuwan da ya kamata yayi
Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sallami hafsoshin tsaro da suka dade kan mulki.
Yan majalisan sun yanke wannan shawara na aikewa Buhari sakon ne sakamakon kudirin da Sanata mai wakiltar Borno ta tsakiya, Kashim Shettima, ya gabatar gaban majalisa.
Wannan bukata ya zo watanni shida bayan majalisar ta bukaci hafsoshin tsaro suyi murabus daga kujerunsa saboda sun gaza.
Hafsoshin tsaron da ya kamata a ce tuni sun yi ritaya amma shugaba Buhari ke cigaba da amfani sune shugabansu, Janar Gabriel Olonisakin; shugaban sojin kasa, Laftanan Janar Tukur Buratai; Shugaban Mayakan Sama, Air Marshal Sadique Abubakar da shugaba Sojin ruwa, Ibok-Ete Ekwe Ibas.
Shettima ya janyo hankalin Sanatocin ne zuwa kisan manoma 45 da aka yi a kauyen Kwashabe, wani gari dake da nisan kilomita 20 da birnin jihar Borno, Maiduguri.
A karshen zaman majalisa na ranar Talata, 1 ga watan Disamba, yan majalisan sun yi ittifakin cewa:
"Majalisa na kira ga gwamnatin tarayya tayi gaggawan shirye-shiryen cire hafsoshin tsaro da suka wuce wa'adinsu, kuma a mayesu da sabbi masu sabbin tunani da mafita."
KU KARANTA: Majalisar dattawa ta tabbatar Farfesa Mahmood Yakubu matsayin shugaban INEC
KU DUBA: An ragewa Kwamandan Operation Lafiya Dole matsayi don yayi kukan rashin makamai
A bangare guda, Garba Shehu, babban mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kafofin watsa labarai, ya ce kiraye-kiraye da ake yi na a sallami shugabannin tsaro baya kan layi.
A cewar Shehu, Shugaban kasar na da ikon nadawa ko sallamar shugabannin tsaro, inda ya kara da cewa Shugaban kasar na ajiye shugabannin tsaro idan har ya gamsu da kokarinsu.
Da yake martani ga kiraye-kirayen yan Najeriya wadanda ke so a sauya fasalin tsaron kasar, Shehu ya ce shawarar sallama ko ci gaba da barin kowani shugaban tsaro ya rataya ne a kan wuyan Shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng