Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da Farfesa Mahmood Yakubu matsayin shugaban INEC

Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da Farfesa Mahmood Yakubu matsayin shugaban INEC

- Bayan makonni da zabensa, majalisa ta amince Farfesa Mahmoud Yakubu ya cigaba da gashi

- Farfesa Yakubu ya gaji Farfesa Attahiru Jega wanda yayi wa'adi daya kacal

- An tabbatar da shi duk da barazanar Sanatocin jam'iyyar PDP

Majalisar dattawa a ranar Talata ta tabbatar da nadin Farfesa Mahmood Yakubu, a matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa INEC na karin shekaru biyar.

Tabbatar da shi ya biyo bayan rahoton da kwamitin majalisar dattawa kan INEC karkashin jagorancin Sanata Kabiru Gaya, ta gabatar a zauren majalisa kuma aka bukaci a amince da shi.

Sanatocin sun siffanta Farfesa Yakubu a matsayin wanda ya cancanci cigaba da zama shugaban hukumar.

KU DUBA: An ragewa Kwamandan Operation Lafiya Dole matsayi don yayi kukan rashin makamai

Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar Farfesa Mahmood Yakubu matsayin shugaban INEC
Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar Farfesa Mahmood Yakubu matsayin shugaban INEC Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Mun kawo muku cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi Farfesa Maumoud Yakubu domin zama shugaban hukumar zabe ta kasa watau INEC karo na biyu, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanto a zauren majalisa.

Shugaban kasan ya bukaci majalisar tayi gaggawar tabbatar da Farfesa Yakubu saboda ya kara shekaru 5 a INEC.

Buhari ya bayyana hakan ne a wasikar da ya aike majalisar, kuma shugaban majalisar Ahmad Lawan ya karantawa Sanatacoi ranar Talata, 24 ga Nuwamba, 2020.

KU KARANTA: Majalisar dattawa ta bukaci Buhari ya sallami Buratai, Sadiqu Baba, dss

Sanatocin jam’iyyar adawa ta PDP a majalisar dattawa sun shirya domin hana a amince da sabon wa’adin Farfesa Mahmood Yakubu a hukumar INEC.

Jaridar This Day ta ce ‘yan adawan da ke majalisar tarayyar ba su goyon bayan Mahmood Yakubu ya sake shafe wasu shekaru biyar ya na rike da hukumar.

Hakan na zuwa ne bayan ‘yan majalisar tarayya sun dawo daga hutun da su ka je, yanzu an cigaba da sauraron zaman kare kasafin kudin shekarar badi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel