Yanzu-yanzu: Lauyan Maina ya yi watsi da shi, ya janye daga kareshi a kotu
- Bayan damkeshi da akayi a Nijar, da alamun AbdulRashid Maina ya shiga tsaka mai wuya
- Lauyan da ke kareshi a kotu ya fadawa Alkali cewa har yanzu ba'a biyashi kudin aikinsa ba
Babban kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta baiwa Mr Adeola Adedipe daman janyewa daga shari'ar almundahana da ake yiwa tsohon shugaban kwamitin fansho, AbdulRashid Maina.
A zaman kotun da akayi ranar Alhamis a Abuja, Alkali kong Abang ya biwa lauyan daman zame kansa saboda har yanzu wanda ya daukeshi aiki bai biya shi kudin aikinsa ba kuma bai san inda yake ba, NewsWireNGR ta ruwaito.
Ana cigaba da gurfanar da AbdulRashid Maina ne kan zargin rub da ciki da kudi bilyan biyu da hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa ke masa.
KU DUBA: Dattawan arewa na nan akan bakarsu na neman Buhari ya sauka, In ji Hakeem Baba Ahmed
Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana shirye-shiryen dawo da tsohon shugaban kwamitin gyaran hukumar fanshi, AbdulRashid Maina, wanda aka damke a birnin Niamey, jamhuriyyar Nija, ranar Litinin.
Hadakar hukumar yan sandan Najeriya da na INTERPOL sun damkeshi ne bayan guduwa da yayi daga Najeriya.
Yanzu haka yana tsare a hannun hukumomin Nijar kafin a dawo da shi.
Kakakin hukumar yan sandan Najeriya, Frank Mba, a jawabin da ya saki ranar Talata yace hukumar na kokarin ganin an dawo dashi.
KU KARANTA: Kin sallaman Buratai da takwarorinsa, Buhari na karya doka: Malam Ibrahim Shekarau
A ranar 18 ga Nuwamba, 2020, Alkali Abang ya janye belin da ya baiwa Maina kuma ya bada umurnin daureshi.
Bayan an nemi Maina an rasa, Alkali ya ce a garkame Ndume a kurkuku maimakonsa ko ya biya kudi N500m.
Bayan kwana hudu da tsare Ndume, Alkali Abang ya bada belin Sanatan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng