Kada a saki jiki, har yanzu akwai Korona, 281 suka kamu jiya Talata

Kada a saki jiki, har yanzu akwai Korona, 281 suka kamu jiya Talata

- An fara sha'afa kan lamarin annobar Korona yayinda daruruwan yan Najeriya na sake kamuwa da cutar kulli yaumin

- Gwamnatin tarayya na tsoron adadin masu kamuwa da cutar zai yi tashin gwauron zabi saboda abinda ke faruwa a nahiyar Turai

- Hukumar NCDC ta bayyana adadin wadanda suka kamu da cutar ranar Talata a fadin tarayya

Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus 281 ranar Talata a cewar hukumomin kiwon lafiya.

Adadin da aka samu ranar Talata ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 67,838 a Najeriya.

Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da hakan a daren Talata , 2 ga watan Disamba, 2020.

Yayinda adadin masu kamuwa ke raguwa, adadin masu samun waraka daga cutar na kara yawa.

Daga cikin mutane kimanin 68,000 da suka kamu, an sallami 63,430 yayinda 1176 suka rigamu gidan gaskiya.

KU KARANTA: Buhari ne babban matsalan Najeriya a yau, cewar gamayyar kungiyoyin Arewa

Kada a saki jiki, har yanzu akwai Korona, 281 suka kamu jiya Talata
Kada a saki jiki, har yanzu akwai Korona, 281 suka kamu jiya Talata Credir: NCDCGov
Source: Twitter

Ga jerin adadin wadanda suka kamu a jihohin Najeriya:

Lagos-123

FCT-64

Kaduna-38

Imo-15

Rivers-11

Plateau-8

Ogun-5

Bayelsa-4

Kwara-4

Bauchi-3

Edo-3

Kano-2

Osun-1

KU DUBA: Kayi murabus yanzu: Buhari na fuskantar matsin lamba yayinda dattawan arewa suka tunzura kan kisan Zabarmari

Ministan birnin tarayya Abuja, Muhammadu Musa Bello, ya bayyanawa majalisar dattawan tarayya cewa ya kashe kimanin bilyan 29 domin dakile cutar Korona a Abuja.

Yayin jawabi ga mambobin kwamitin birnin tarayya na majalisar dattawa, Ministan yace an kashe kudaden ne wajen inganta tsaro, kayan abincin rage radadin Korona, da kuma jihohin dake makwabtaka mabukata.

Ya kara da cewa gwamnatin Abuja ta taimakawa mazauna birnin da makwabta da kayayyakin kiwon lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel