Buhari ne babban matsalan Najeriya a yau, cewar gamayyar kungiyoyin Arewa

Buhari ne babban matsalan Najeriya a yau, cewar gamayyar kungiyoyin Arewa

- Matasan Arewa sun yi alhinin tabarbarewan tsaro a Arewa Najeriya

- A makon da ya gabata yan Boko Haram suka hallaka manoma 73 a jihar Borno

Gamayyar kungiyoyin Arewa a ranar Talata ta yi Alla-wadai da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan yadda rashin tsaro ya tabarbare a Arewacin Najeriya.

A jawabin da Kakakin gamayyar, Abdul-Azeez Sulaiman, ya saki, ya ce Arewacin Najeriya yanzu ta zama filin yaki saboda yan Boko Haram, masu garkuwa da mutane, barayin shanu da masu fyade, wadanda ke cin karkukansu ba babbaka.

Kungiyar ta tuhumi shugabannin Arewa da masu fada aji, da daukan abinda ke faruwa wasa saboda su da iyalansu na wurare masu lumana.

Sulaiman ya ce kungiyar na kira ga mazauna Arewa su cigaba da addu'a Allah ya kawo sauyi kuma su shirya kare kawunansu.

"Mu a Arewa, tsare rayukan mutane ne babban matsalanmu. Ba zamu yi tsauri ba idan muka ce Buhari ne babbar matsalan Najeriya a yau," jawabin yace.

"Kowa ya ji abinda ya faru a Zabarmari ne saboda adadin wadanda aka kashe na da yawa kuma ya faru a waje daya."

"Amma gaskiyar magana itace irin haka na faruwa kusan ko ina a Arewa saboda yankin ta zama tamkar filin yaki yanzu, karkashin mulkin Boko Haram, masu garkuwa da mutane, barayin shanu da masu fyade, wadanda ke yawo yadda suka ga dama yayinda shugaba Buhari da gwamnatinsa ke cigaba da karyatawa."

KU KARANTA: Mun kashe N28.5bn kan cutar Korona a Abuja, Ministan FCT Musa Bello

Buhari ne babban matsalan Najeriya a yau, cewar gamayyar kungiyoyin Arewa
Buhari ne babban matsalan Najeriya a yau, cewar gamayyar kungiyoyin Arewa Hoto: Presidency
Asali: Twitter

KU DUBA: Kayi murabus yanzu: Buhari na fuskantar matsin lamba yayinda dattawan arewa suka tunzura kan kisan Zabarmari

A bangare guda, majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sallami hafsoshin tsaro da suka dade kan mulki.

Yan majalisan sun yanke wannan shawara na aikewa Buhari sakon ne sakamakon kudirin da Sanata mai wakiltar Borno ta tsakiya, Kashim Shettima, ya gabatar gaban majalisa.

Wannan bukata ya zo watanni shida bayan majalisar ta bukaci hafsoshin tsaro suyi murabus daga kujerunsa saboda sun gaza.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel