EFCC ta sake gurfanar da Babachir a gaban sabon alkali a kan kwangilar cire shu'umar ciyawa a kan N544m

EFCC ta sake gurfanar da Babachir a gaban sabon alkali a kan kwangilar cire shu'umar ciyawa a kan N544m

- A karo na farko tun bayan mutuwar Jastis Jude Okeke, EFCC ta sake gurfanar da Babachir David Lawal

- An fara gurfanar da Bachir, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, a watan Fabarairu na shekarar 2019

- EFCC na tuhumar Babachir da yin amfani da ofishinsa wajen bawa kamfaninsa kwangilar cire ciyawa a kan N544m

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta sake gurfanar da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, tare da sauran wasu mutane Shidda, bisa zarginsu da badakalar N544m.

EFCC ta na zargin Babachir, da sauran mutanen, da yin amfani da matsayinsa wajen bawa kamfaninsa kwangilar cire wata shu'umar ciyawa a sansanin 'yan gudun hijira (IDP) a kan kudi har miliyan N544.

Sai dai, Babachir da sauran mutanen da aka gurfanar sun ce basu aikata laifukan da ake tuhumarsu da su ba a cikin takardar kara da aka karanta a gaban Jastis Charles Agbaza, alkalin babbar kotun tarayya da ke Jabi a Abuja.

KARANTA: An cire kwamandan bataliyar sojojin da ke Zabarmari bayan kisan manoma 43

Wannan shine karo na biyu da aka gurfanar da Babachir da sauran wadanda ake tuhuma bayan mutuwar Jastis Jude Okeke, tsohon alkalin da ke sauraron karar, wanda ya mutu ranar 4 ga watan Agusta, 2020.

EFCC ta sake gurfanar da Babachir a gaban sabon alkali a kan kwangilar cire shu'umar ciyawa a kan N544m
EFCC ta sake gurfanar da Babachir a gaban sabon alkali a kan kwangilar cire shu'umar ciyawa a kan N544m @Channels
Asali: Twitter

An fara gurfanar da Babachir, dan uwansa; Hamidu Lawal, Apeh Monday, da wasu kamfani guda biyu, a gaban marigayi Jastis Okeke a ranar 13 ga watan Fabarairu na shekarar 2019.

A ranar da aka fara zama domin fara sauraron shari'ar a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2019, lauya mai gabatar da kara ya bukaci kotu ta bashi lokaci domin sake tsara jadawalin tuhuma 10 da ake yi wa Babachir dangane da badakalar kwangilar N544m.

KARANTA: Korafi: Pantami ya dauki alkawarin isar da sakon 'yan arewa ga Buhari

Hukumar EFCC ta fara kiran shaidunta a gaban kotu bayan ma su laifi sun yi gardamar amsa laifukansu.

Sai dai, kafin a kammala zaman sauraron gabatar da shaidun ne sai Jastis Okeke ya rasu.

Bayan rasuwar Jastis Okeke ne sai aka mayar da sharia'ar hannun Jastis Agbaza wanda ya fara sauraron shari'ar a karon farko ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, an dawo da wani tsohon bidiyo da shugaba Buhari ke zargin gwamnatin tarayya da zama babbar mai daukar nauyin kungiyar Boko Haram.

Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke takara, gabanin zaben shekarar 2015.

Dawo da bidiyon tamkar tuni ne ga shugaba Buhari domin ya tuna alakwuran da ya daukarwa 'yan Najeriya yayin yakin neman zabe.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel