Waiwaye: Bidiyon kalaman Buhari a kan yadda FG ke daukar nauyin kungiyar Boko Haram kafin ya hau mulki

Waiwaye: Bidiyon kalaman Buhari a kan yadda FG ke daukar nauyin kungiyar Boko Haram kafin ya hau mulki

- Ayyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram sun fara bayyana ne tun cikin shekarar 2009 a jihar Borno

- Har yanzu, bayan fiye da shekaru 10, kungiyar Boko Haram ba ta daina kai hare-hare tare da kami'an tsaro da fararen hula ba

- Buhari ya samu nasarar lashe zaben shekarar 2015 bisa tsammanin da jama'a a ke yi a kan cewa zai kawo karshen matsalar

A yayin da jama'a a Najeriya, musamman mazauna yankin arewa, ke juyayin kisan manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a jihar Borno, Legit.ng ta yi waiwaye adon tafiya a kan wani tsohon faifan bidiyo.

Matsalar Boko ta dade ta na ci wa gwamnatin Najeriya tuwo a kwarya, kusan duk wani yunkuri na kawo karshen matsalar ya ci tura.

Gaza kawo karshen matsalar Boko Haram na daga cikin dalilan da suka jawo faduwar gwamnatin PDP a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan.

Waiwaye: Bidiyon kalaman Buhari a kan yadda FG ke daukar nauyin kungiyar Boko Haram kafin ya hau mulki
Waiwaye: Bidiyon kalaman Buhari a kan yadda FG ke daukar nauyin kungiyar Boko Haram kafin ya hau mulki @Thecable
Asali: Twitter

A lokacin da ya ke yakin neman zabe, shugaba Buhari ya sha daukan alkawarin cewa zai tabbatar da tsaro tare da kare dukkan 'yan kasa daga wata barazanar tsaro.

KARANTA: An cire kwamandan bataliyar sojojin da ke Zabarmari bayan kisan manoma 43

A wata hira da aka yi da shi, wacce Channels TV ta nada kafin zaben shekarar 2015, shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ce ta ke daukan nauyin Boko Haram tunda ta gaza kawo karshen kungiyar.

"gwamnatin tarayya ce, da kanta, babbar mai daukar nauyin Boko Haram, saboda tana da dukkan ikon dakatar da mulkin mulikiyya da duk wani rikicin na siyasa," kamar yadda Buhari ya bayyana a cikin bidiyon.

KARANTA: Bidiyo: Sheikh Daurawa ya bayyana yadda ake wulakanta Malamai idan sun so ganin Buhari domin yi masa nasiha

A baya Legit.ng ta wallafa rahoton cewa tsohon dan majalisa a Jamhuriya ta biyu, Dattijo Dakta Mohammed Junaid, ya ce ba za'a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba matukar shugaba Buhari da APC suna kan mulki.

A cewarsa, batun gyaran Najeriya fa ya fi karfin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Dakta Junaid ya bayyana hakan ne yayin da yake martani a kan kisan manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a ranar Asabar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng