Da duminsa: An cire kwamandan bataliyar sojojin da ke Zabarmari bayan kisan manoma 43

Da duminsa: An cire kwamandan bataliyar sojojin da ke Zabarmari bayan kisan manoma 43

- Rahoto da dumi-duminsa daga jaridar HumAngke na nuni da cewa an sauya kwamandan bataliyar sojoji da ke Zabarmari

- Batun kisan manoma 43, da mayakan kungiyar Boko Haram suka yanka, a kauyen Zabarmari ya tayar da hankulan jama'a

- Jama'a da dama, musamman 'yan arewa, sun mamaye dandalin sada zumunta da alhinin kisan manoman

Mahukunta a sashen rundunar soji da ke kula da mayar da martani ga 'yan ta'adda ya cire kwamandan bataliyar soji da aka jibge a Zabarmari da ke yankin karamar hukumar Jere a jihar Borno, kamar yadda HumAnge ta rawaito.

A jiya, asabar, ne rahotanni suka bayyana cewa ƴan Boko Haram sun shiga ƙauyen Zabarmari, sun bi manoma har gonakinsu tare da hallakasu ta hanyar yi musu yankan rago.

Zabarmari kauye ne mai nisan kilomita 20 kacal daga hedikwatar rundunar atisayen Lafiya Dole wacce ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

An jibge bataliyar soji ta 195 a yankin Zabarmari domin mayar da martanin gaggawa a lokutan harin mayakan kungiyar Boko Haram.

KARANTA: 'Yan ta'adda sun tashi sinadarai masu fashewa a Cocin mahaifin gwamna Wike

Da duminsa: An cire kwamandan bataliyar sojojin da ke Zabarmari bayan kisan manoma 43
Da duminsa: An cire kwamandan bataliyar sojojin da ke Zabarmari bayan kisan manoma 43 @Premiumtimes
Asali: Twitter

HumAngle ta ce ta fahimci cewa sabon kwamandan da aka tura zai jagoranci binciken neman gawar saura manoma da mayakan kungiyar Boko Haram suka yanka a gonakinsu na shinkafa.

KARANTA: Da sauran rina a kaba: ASUU ta yi karin haske a kan rahotannin janye yajin aiki

Majalisar dinkin duniya (UN) ta rawaito cewa a kalla mutane 110 aka kashe, lamarin da ke nuni da cewa an samu karuwar adadin mutanen daga 43 da aka rahotanni suka fara sanarwa.

Ana zargin cewa bayan kisan manoman, mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da mata ma su yawa.

"Wasu mutane dauke da makamai sun kai hari a kan fararen hula maza da mata yayin da suke girbe amfanin da suka shuka a gonakinsu," a cewar Edward Kallon, shugaban ayyukan UN na ceto a Najeriya.

."Wannan shine hari mafi girma da mayakan Boko Haram suka kaddamar a kan fararen hula a cikin shekarar nan. Ina kiran a tabbatar da cewa wadannan miyagu sun shiga hannu domin su fuskanci hukunci," kamar yadda Kallon ya bayyana a cikin jawabin da ya fitar ranar Lahadi.

Miyagun 'yan ta'addar sun daure manoman kafin su yankasu, sannan sun kone gonakin manoman da kayan amfanin da aka noma.

Batun kisan ya hasala jama'a, lamarin da yasa da dama suka yi kira a kan gwamnati ta rubanya kokarinta na kawo karshe ayyukan ta'addanci a arewacin Najeriya.

A cikin sakon alhinin kisan manoman da ya fitar ta hannun kakakinsa, shugaba Buhari ya ce gwamnatin tarayya "ta bawa hukumomin tsaro dukkan abin da suke da bukata domin kare kasa da jama'arta a duk inda suke."

Dangane da batun kisan ne Legit.ng ta rawaito cewa wasu ma'abota amfani da dandalin sada zumunta na tuwita sun roki ministan sadarwa, Dakta Isa Pantami, ya isar da sakonsu ga Buhari.

Pantami ya ce zai miƙa saƙonnin jama'a ga Shugaban ƙasa Muhammad Buhari bisa kisan gillar da ƴan Boko Haram suka yi na manoma 43.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel