Minista: Miliyan N81 ma'aikatar wasanni ke bukata domin sassabe ciyawa filin wasan Abuja

Minista: Miliyan N81 ma'aikatar wasanni ke bukata domin sassabe ciyawa filin wasan Abuja

- Sunday Dare, ministan wasanni, ya ce ma'aikatar wasanni ta na bukatar miliyan N81 domin cire ciyawa daga filin wasa na MKO Abiola

- A cewar ministan, hukumar kula da muhalli ta Abuje ce ta bukaci ma'aikatar wasanni ta biya kudaden domin a cire musu ciyawar

- Ministan ya ce ma'aikatar wasanni ba ta da adadin kudaden da hukumar kula da muhallin ta nema domin gudanar da aikin

Ministan matasa da cigaban wasanni, Sunday Dare, ya bayyana cewa zai ɗauki ma'aikatarsu miliyan ₦81 don gyara da cire ciyayin da ba'a buƙata a babban filin wasa na ƙasa 'MKO Abiola' da ke Abuja.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana a wurin taron ƙarawa juna sani wanda ƙungiyar marubutan wasanni [SWAN] reshen Abuja suka haɗa.

A cewarsa, ma'aikatarsa ta tunkari Hukumar kare Muhallin Abuja (AEPB) don kimanta abin da aikin filin zaici.

KARANTA: 'Yan ta'adda sun tashi sinadarai masu fashewa a Cocin mahaifin gwamna Wike

Filin, wanda aka gina shi a shekarar 2003, a wuri mai faɗin hekta 29(72 acres) na ƙasa, ya lashe Naira biliyan ₦53.

Minista: Miliyan N81 ma'aikatar wasanni ke bukata domin sassabe ciyawa filin wasan Abuja
Minista: Miliyan N81 ma'aikatar wasanni ke bukata domin sassabe ciyawa filin wasan Abuja
Source: UGC

An raba filin wasan zuwa ɓangarori biyu wato ɓangaren A wanda ke ɗauke da gundarin filin, sai ɓangaren B wanda yake ɗauke da filin ƙwallon kwando, ofishin NFF, filin ƙwallon raga da sauransu.

KARANTA: Da sauran rina a kaba: ASUU ta yi karin haske a kan rahotannin janye yajin aiki

"Mun tunkari hukumar kula da muhallin Abuja(AEPB) su zo su ga abin da za'a yi don cire ciyayin da sauran muggan ciyayi, sai suka ce mana za su caje mu kuɗi har miliyan ₦81.

"Idan muka gayawa ƴan Najeriya mun yi amfani da miliyan ₦81 wadda bamu da ita, za ka ji hargowar mutane.

"Ba mu da kuɗaɗen, wannan shine dalilin da yasa muke haɗa hannu da masu zuba hannayen jari masu zaman kansu, don farfarɗo da kayayyakin aikinmu," a cewarsa.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa Dakta Isa Pantami, ministan Sadarwa da tattalin arziƙin fasahar yanar gizo, ya ce zai miƙa saƙonnin jama'a ga Shugaban ƙasa Muhammad Buhari bisa kisan gillar da ƴan Boko Haram suka yi na manoma 43.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel