Da sauran rina a kaba: ASUU ta yi karin haske a kan rahotannin janye yajin aiki

Da sauran rina a kaba: ASUU ta yi karin haske a kan rahotannin janye yajin aiki

- Tun watan Maris na farkon shekarar 2020 kungiyar ASUU ta fara yajin aiki

- Wakilcin gwamnatin tarayya da shugabancin kungiyar ASUU sun yi zama babu adadi domin kawo karshen yajin aikin

- A yayin da rahotannin ranar Juma'a ke nuna cewa ASUU ta janye yajin aikin, shugaban kungiyar ya musanta hakan

Kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta musanta rahotannin da ake yadawa a kan cewa ta amince za ta janye yajin aikin da ta shafe fiye da watanni takwas ta na dakawa.

A ranar Juma'a ne kafafen yada labarai suka fara wallafa rahotannin cewa ASUU za ta janye yajin aiki bayan ganawar shugabancin kungiyar da tawagar gwamnatin tarayya a karkashin ministan kwadago da samar da ayyuka, Sanata Chris Ngige.

Yayin tattaunawarsu a ranar Juma'a, wacce aka yi a dakin taro na ma'aikatar kwadago, FG ta karawa ASUU biliyan N5 a kan biliyan N65 da ta fara yi mata tayi.

KARANTA: Bauchi: 'Yan sanda sun yi ram da Sadiya Kaura, matashiyar da ke bawa 'yan fashi da barayi mafaka

A cikin makon da ya gabata ne FG ta amince da cire ASUU daga tsarin IPPIS na biyan albashin ma'aikatanta tare da basu biliyan N65 domin biyan bashin al albashi da alawus din malaman jami'o'i.

Da sauran rina a kaba: ASUU ta yi karin haske a kan rahotannin janye yajin aiki
Da sauran rina a kaba: ASUU ta yi karin haske a kan rahotannin janye yajin aiki
Asali: Twitter

Yayin tattaunawar da suka gudanar ranar Juma'a, ASUU ta nuna alamun za ta iya jingine yajin aikin da ta fara tun watan Maris bayan FG ta amince da kara adadin kudaden da ta bayar zuwa N70bn daga N65bn.

FG ta ce za ta bawa ASUU N70bn; N40bn a matsayin biyan bashin albashi da alawus din malaman jami'o'i da kuma N30bn domin farfado da kima da darajar jami'o'i.

KARANTA: Tabarbarewar tsaro: Nigeria ta zama kasa ta uku mafi shahara a ta'addanci a duniya

Sai dai, shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya musanta cewa kungiyar ta cimma yarjejeniyar janye yajin aikin.

A cewarsa, kungiyar ASUU ta amince ne a kan cewa za ta sanar da sassa da rassan kungiyar sakamakon tattaunawarta da FG kafin sanar da mataki na gaba.

Sanata Ngige, bayan kammala ganawar, ya ce tattaunarsu da ASUU ta yi armashi matuka, inda ya ce kungiyar za ta tuntubi mambobinta kafin sanar da FG matsayar da suka cimma dangane da janye yajin aikin ko akasin hakan.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa gwamnatin tarayya a ranar Juma'a ta cigaba da tattaunawa da kungiyar malaman jami'o'inNajeriya ASUU domin kawo karshen yajin aiki wata takwas dake gudana.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng