Rashin tsaro: Dattawan Arewa sun jinjinawa Sarkin Musulmi bisa jawabin da yayi

Rashin tsaro: Dattawan Arewa sun jinjinawa Sarkin Musulmi bisa jawabin da yayi

- Sarkin Musulmi ya bayyana cewa Arewacin Najeriya ne wuri mafi hadarin zama yanzu

- Wasu dattawan Arewan sun ce lallai gaskiya mai alfarma a fadi

- Sun yi kira ga sauran shugabannin Arewa su bude mukulle bakinsu su tofa nasu albarkacin

Dattawan Arewa sun jinjinawa mai alfarma sarkin Musulumi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, kan abind asuka siffanta matsayin fadin gaskiya kan lamarin tsaro ya tabarbare a yankin.

A cewar dattawan, matsayar Sarkin Musulmi ne gaskiyar magana kan rashin tsaro a Arewa, kuma shine musababbin matsalar tsadar abinci da ake fama da shi a kasar gaba daya.

Dattawan karkashin gamayyar dattawan Arewa wajen neman zaben lafiya da cigaba, a jawabin da suka saki ranar Asabar, sun ce Sarkin Musulmi ya fiddasu kunya kan lamarin tsaro a yankin.

Shugaban gamayyar, Injiniya Zanna Goni da shugaban mata, Hajia Mairo Bichi, ne suka rattafa hannu kan jawabin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Saboda haka, dattawan sun yi kira ga sauran shugabannin Arewa su sanya baki kan fadin gaskiyar abinda ke faruwa a yanzu domin janyo hankalin hukumomi.

Musamman, sun yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya yi sauye-sauye a lamarin tsaron kasar nan, domin samun sakamako mai kyau.

Jawabin yace: "Muna masu yabawa Sultan na Sokoto, mahaifinmu, kan fayyace gaskiyan abubuwan da ke faruwa a Arewa, kan tsaro."

"Muna kara jaddadawa, lamarin tsaro yayi munin da manomanmu ba sa iya zuwa gonakinsu, har matafiya ba sa iya tafiya cikin kwanciyar hankali saboda tsoron masu garkuwa."

KU KARANTA: Ku bamu mako daya domin ganin yiwuwar rage farashin mai, gwamnatin tarayya ga kwadago

Rashin tsaro: Dattawan Arewa sun jinjinawa Sarkin Musulmi bisa jawabin da yayi
Rashin tsaro: Dattawan Arewa sun jinjinawa Sarkin Musulmi bisa jawabin da yayi
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta bude shafin daukan tsaffin ma'aikatan N-Power a CBN

Mun kawo muku cewa Sarkin Musulmi, ya yi Alla-wadai da lamarin tsaro ya tabarbare a Arewacin Najeriya, inda yace yan bindiga na cin karansu ba babbaka.

Sarkin Musulmi wanda shine shugaban majalisar koli ta lamuran addini a Najeriya ya bayyana cewa yanzu yan bindiga gida-gida suke bi suna awon gaba da mutane a Arewa.

Alhaji Sa'ad ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, yayin taron majalisar hadin kan addinai NIREC da akayi a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Sultan yace: "Ba wai babu shawari bane ko babu yadda za'a magance matsalolin ba. Kawai abinda muka rasa shine rashin niyya."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel