Gwamnatin tarayya ta bude shafin daukan tsaffin ma'aikatan N-Power a CBN

Gwamnatin tarayya ta bude shafin daukan tsaffin ma'aikatan N-Power a CBN

- Ma'aikatan Hajiya Sadiya ta samar da shafin samawa matasan N-Power tallafi daga CBN

- Ministar ta yi kira ga matasan da aka cire daga tsarin su ganimci wannna dama

Gwamnatin tarayya ta bude sabon shafin da zai taimakawa tsaffin matasan N-Power dman neman tallafi da jari na babban bankin Najeriya CBN, rahoton Leasership.

Wannan shafi da ma'aikatar jinkai da walwala ta shirya tare da hadin kan CBN zai taimakawa wadanda aka cire daga shirin N-Power su shiga domin neman abubuwan alfanu da CBN ke da shi na tallafi, bashi da jari.

A jawabin da Sakataren ma'aikatar, Bashir Nura Alkali ya sake a madadin ministar, Hajiya Sadiya Farouq, ta yi kira ga matasan su shiga shafin domin sanya sunayensu saboda su samu shiga cikin duk wani shiri da CBN ta gabatar.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Dattawan Arewa sun jinjinawa Sarkin Musulmi bisa jawabin da yayi

Gwamnatin tarayya ta bude shafin daukan tsaffin ma'aikatan N-Power a CBN
Gwamnatin tarayya ta bude shafin daukan tsaffin ma'aikatan N-Power a CBN
Asali: UGC

"An bude shafin NEXIT ne domin ganin inda matasan N-Power zasu samu shiga a shirye-shiryen CBN kuma sai mutum ya cika sharrudan wadannan da CBN ta kindaya," cewar Minista Sadiya.

Ministar ta mika godiyarta ga gwamnan CBN, Godwin Emefiele kan wannan taimako.

Hajiya Sadiya ta yi alkawarin cewa ma'aikatarta za ta cigaba da hada kai da wasu ma'aikatun gwamnati da masu ruwa da tsaki wajen ganin an cimma manufar shugaba Buhari na tsamo mutane milyan 100 daga cikin talauci.

KU KARANTA: Ku bamu mako daya domin ganin yiwuwar rage farashin mai, gwamnatin tarayya ga kwadago

A bangare guda, kungiyar yan kasuwa masu masu yaƙi da COVID-19 (CACOVID) a Najeriya, sun sanar da bayanan cigaban ayyukansu da kuma niyyarsu ta tallafawa gwamnati a ƙoƙarin sake gini don farfaɗo da tattalin arziƙin kasar.

Hakan ya biyo bayan tashin hankalin da ƴan daba waɗanda suka gwace ragamar zanga-zangar EndSARS suka haddasa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Zanga-zangar wadda ta jawo asarar rayuka ,dukiyoyi da tsayawar al'amura cak a jihohin da abin ya shafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel