Yanzu yan bindiga gida-gida suke bi suna diban mutane, Sarkin Musulmi

Yanzu yan bindiga gida-gida suke bi suna diban mutane, Sarkin Musulmi

- Sarkin Musulmi ya yi alhinin tabrbarewar tsaro a yankin Arewacin Najeriya

- Sarki Sa'ad yace shugabannin kasar basu da niyyar gyara ne kawai

- Sultan Sa'ad dai tsohon jami'in Soja ne kafin yayi murabus ya zama shugaban NSCIA

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar II, ya yi Alla-wadai da lamarin tsaro ya tabarbare a Arewacin Najeriya, inda yace yan bindiga na cin karansu ba babbaka.

Sarkin Musulmi wanda shine shugaban majalisar koli ta lamuran addini a Najeriya ya bayyana cewa yanzu yan bindiga gida-gida suke bi suna awon gaba da mutane a Arewa.

Alhaji Sa'ad ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, yayin taron majalisar hadin kan addinai NIREC da akayi a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Sultan yace: "Yanzu nawa albasa a kasuwa a Najeriya, wannan zai fada maka irin halin kakanikayen da ake ciki a kasar."

"Ba wai babu shawari bane ko babu yadda za'a magance matsalolin ba. Kawai abinda muka rasa shine rashin niyya."

KU KARANTA: Kada a bude boda, zamu wahala, kungiyar manoma ga shugaba Buhari

Yanzu yan bindiga gida-gida suke bi suna diban mutane, Sarkin Musulmi
Yanzu yan bindiga gida-gida suke bi suna diban mutane, Sarkin Musulmi Hoto: Presidency
Source: Twitter

A cikin 'yan kwanakin jami'ar ABU Zariya ta na fuskantar barazana bayan an sace wata malamar asibiti da kuma wani Farfesa a sashen koyar da aikin likitanci.

Bayan haka, masu garkuwa da mutane sun shiga makarantar Nuhu Bamalli, sun sace wani malami da yara biyu, an harbi wani Bawan Allah a dalilin harin.

KU KARANTA: Hukumar Soji ta karawa marigayi Kanal Bako girma zuwa Birgediya Janar don karramashi

Hakan ya sa a ranar Laraba, 26 ga watan Nuwamba, 2020, majalisar wakilan tarayya ta koka game da matslar rashin tsaro da yake kara yaduwa a yankunan kasar nan.

Jaridar Punch ta ce majalisa ta yi wannan magana ne a dalilin hare-haren da aka kai a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da wasu makarantu a kasar.

Majalisar wakilan ta bukaci gwamnatin tarayyya, ‘ba tare da bata lokaci ba’, ta kafa katanga da zata zagaye jami’ar ABU kamar yadda aka yi a wasu jami’o’i.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel